Jam’iyyar APC: A gyaran gira, za a rasa ido

A makonnin da suka gabata ne tawagar jam’iyyar APC, karkashin jagorancin Janar Muhammadu Buhari suka kai wata ziyarar bazata, wadda aka yi wa lakabi da (zawarcin Gwannoni 7). Zawarcin ya fara ne da garin Kano, inda suka kai ziyarar a gidan Gwamnatin Kano, daga nan sai suka wuce Jigawa, nanma sun isa gidan Gwamnatin Jigawa […]

Jam’iyyar APC: A gyaran gira, za a rasa ido

A makonnin da suka gabata ne tawagar jam’iyyar APC, karkashin jagorancin Janar Muhammadu Buhari suka kai wata ziyarar bazata, wadda aka yi wa lakabi da (zawarcin Gwannoni 7). Zawarcin ya fara ne da garin Kano, inda suka kai ziyarar a gidan Gwamnatin Kano, daga nan sai suka wuce Jigawa, nanma sun isa gidan Gwamnatin Jigawa don zawarcin Alhaji sule Lamido.

Hakika tunani da hangen nesan da jam’iyyar ta APC tayi, na neman wasu gwamnoni su shigo cikin ta don a ceto Najeriya daga kangin talauci, fatara, gurguncewar tattalin arziki, tsaro, lafiya da ilimi, ya yi daidai, haka kuma yazo akan lokacin da ya dace.
Sai dai a kokarin gyaran gira ana neman a rasa ido, don a kokarin neman gwamnoni ana neman a rabu da wadanda ake tare da su, ke nan ana neman a yi jifar gafiyar baidu. Idan muka tuna yadda zabubbukan gwamnoni suka gabata na 2011, musamman a Katsina da Kano da Jigawa, kusan za mu ga rashin tsayayyen dan takara ne ya haifar wa jam’iyyar CPC asarar kujerun a wadannan jihohin, don wanda hukumar zabe ta INEC ta ce, shi ne halastaccen dan takara, ba shi ne Jam’iyyar CPC ta ce dan takara ba, kamar a Katsina, INEC ta ce Sanata Yakubu Lado dan Marke (wanda ya koma PDP a yanzu)ne dan takara, ita kuma jam’iyya ta ce tsohon kakakin majalisa, Alhaji Aminu Bello Masari ne dan takara a CPC, wanda hakan ta haifar ma da jam’iyyar asarar kujerar har wata jam’iyya ta dauke. Haka abin yake a Kano, hukumar INEC ta fitar da Mahmud Abacha (wanda ya koma PDP a yanzu) a matsayin dan takarar Gwamnan Kano karkashin jam’iyyar CPC, ita kuma jam’iyya ta fitar da Kanal Jafaru Lawal Isah.
Duk wadannan abubuwan da suke faruwa a jam’iyyar da take da mafiya yawan rinjayen al’ummar Najeriya, da kamata ya yi su hankalta, su dauki darasin da suka san zai kai su ga cimma gaci. Zan so mu fahimci cewar, zawarcin Gwamnoni da jam’iyyar APC ke yi, aikin yana karkashin jam’iyya ne, ba karkashin Janar Muhammadu Buhari ba, shi ya sa masu hangen nesa suka danganta zawarcin da cike yake da kura-kurai, har suke hasashen kada a sake kwata ‘yar gidan jiya.
Masu fashin baki a siyasance, sun ce, mafi dacewar zawarcin duk wani gwamna, to ya biyo ta karkashin ‘yayan jam’iyyar APC (musamman wadanda suka amince aka dunkule guri daya don a ceto Arewa), misali, zuwa Kano bai kamata a mance da su Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau ba, don mafi dacewa, su ya kamata su jagoranci zawarcin Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso a gidan gwamnati, ba wai kawai sai dai su ji jam’iyya ta zo, inda suke ba tare da sanin su ko neman hadin kan su ba.
Hakan tasa wasu kafafen yada labarai ke yada cewar Shekarau yace basu bukatar Kwankwaso a jam’iyyar su ta CPC. Bayan shi kuma Genaral Muhammadu Buhari yana neman da kwankwason ya bar jam’iyyar shi ta PDP, ya dawo CPC. Me wannan ke nufi ke nan?
Haka abin yake a Jigawa, shi ma Faruk Adamu Aliyu wasu kafafen yada labarai sun ruwaito cewar bai da masaniya da zuwan jam’iyyar CPC zawarcin Sule Lamido, har magoya bayan Sule Lamido sun fara yada cewar koda sun koma CPC, suke da wuka da nama.
Dukkan wadannan al’amura da suke ta faruwa a jam’iyyar APC (wadda masu hasashe ke hangen su ke da nasara a zaben 2015) ya samo asali ne da tunanin samun nasara a zaben 2015. Ina mafita?
Ya zama wajibi mu bayar da shawarar ya kamata shugabannin jam’iyyar APC tun daga sama har kasa, da magoya bayan jam’iyyar su cire burbushin jin haushi ko rike wani a rai, dole sai mun yafe ma juna, mu dauka dukkan dan jam’iyya namu ne, mu manta da dukkan abubuwan da suka faru a baya, mu zama tsintsiya daya, mu rika magana da murya daya, mu tunkari kawar da zaluncin da ya murkushe kasar mu.
A karshe mu dage da addu’ar Allah ya ba mu nasara a zaben 2015. ta hakane za mu samu nasarar da muke fatan samu. Gyara kayanka dai bai zama sauke mu raba.
Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi 08095968366.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50