Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa ta jinjina wa Buhari

Jam’iyyar APC reshen Jihar Nasarawa ta yaba da kamun ludayin gwamnatin Shugaban Buhari

Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa ta jinjina wa Buhari

Shugaba Buhari

Jam’iyyar APC reshen Jihar Nasarawa, ta jinjina wa salon shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari a wani taron masu ruwa da tsaki da ta gudanar a Lafiya, babban birnin jihar.

Daya daga cikin shugabannin jam’iyyar a jihar, Mista Mamman Alakayi ya ce, “Wannan taro ne da mazabar Nasarawa ta Kudu ta shirya tana jinjina wa salon shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari.

“Ya samar da sababbin ayyuka a sassan Jihar Nasarawa da suka hada da Kwalejin Horas da ’Yan Sandan Kwantar da Tarzoma a Nasarawa Eggon da Rundunar Sojoji na Musammam a Doma da ta Sojan Sama a Lafiya don inganta harkar tsaro a jihar,” inji shi.

Mammam Alakayi ya ce, taron shi ne na farko a yankin a cikin shekara biyar da suka wuce.

Taron ya kuma yaba da salon shugabancin Gwamna Abdullahi Sule da kuma Sanata Umaru Tanko Al-Makura kan yadda suka ciyar da jihar gaba.

Mahalarta taron sun hada da Mataimakin Gwamnan Jihar, Emmanuel Akabe da Sanata Umaru Al-Makura da Sakataren Gwamnatin Jihar, Aliyu Ubandoma da sauran ’ya’yan jam’iyyar.