Jam’iyyar APC ki sulhunta masu rikici
Anas Saminu Ja’en Makera Hadewar jam’iyyun adawa domin kawar da mulkin zalunci a Najeriya, mataki ne da ya dace, wanda tuni ya kamata a yi shi. Amman akwai wajibcin yin wani shiri na ko ta kwana, ta hanyar hada kan kungiyoyin ‘yan Najeriya masu kishin al’umma da kuma tsoron Allah, marasa kwadayi ko tsoron Wwanda […]
Anas Saminu Ja’en Makera
Hadewar jam’iyyun adawa domin kawar da mulkin zalunci a Najeriya, mataki ne da ya dace, wanda tuni ya kamata a yi shi. Amman akwai wajibcin yin wani shiri na ko ta kwana, ta hanyar hada kan kungiyoyin ‘yan Najeriya masu kishin al’umma da kuma tsoron Allah, marasa kwadayi ko tsoron Wwanda ba Allah, yadda za su zama ginshikin samar da canji daga zalunci zuwa adalci mai dorewa.
Abin takaici shi ne daya daga cikin wadanda suka yi wa jam’iyyar APC takarar gwamna a Kano Hon. Kawu Sumaila A ranar litinin 29-12-2014 da safe ya shaida wa BBC cewa, yadda Gwamna Kwankwaso ke tafiyar da mu’amalarsa ta siyasa da Buhari alamu na nuna cewa tade kafar Buhari yake son yi.
Kawu Sumaila ya bayyana cewa a ba shi takarar mataimakin gwamna a APC ba al’farma bace, kuma ya bayyana cewa sai da wasu mashahuran mutane suka nemi a ba shi mataimakin gwamna bayan an ba shi baki ya hakura da matsayin neman mukamin dan takarar gwamna. Kawu ya ce a cikin wadanda suka nemi a ba shi mataimaki har da janar Buhari, kuma alkawari ne ma aka yi za a ba shi mataimaki bayan an sa ya janye takarar da yake yi.
Kawu ya kara da cewa abin da ya sa Kwankwaso ke jin haushin shi, shi ne, yadda ya hada kan mutane aka zabi Buhari a zaben fidda gwani na shugaban kasa da APC ta yi Legos.
To, amma makusanci ga kwankwaso Ishak Yakasai ya bayyana cewa, ba wanda ya yi wa Kawu alkawarin mataimakin gwamna. Ya kuma kara da cewa dangantakar Buhari da Kwankwaso mai kyau ce har yau. Ya kare da cewa ’yan siyasa sun mayar da Buhari wata hanya ta cin zabe, shi yasa Kawu ya biyo ta wannan kunga idan ku manyan ‘yan siyasa irin su Kawu Sumaila suna fitowa duniya suna fadar irin wadannan maganganu, to tabbas ya zama barazana ga jam’iyyar APC A kano.
Irin wannan rikici na Kano yana faruwa a tsakanin ‘yan takarar gwamna a Jihar Katsina, tsakanin Sanata Kanti Bello da Alhaji Aminu Bello Masari. Abin takaici uwar jam’iyya ta yi shiru duk wadannan mutane suna kiran su talakawa suke son yi wa aiki, me zai hana su hada karfi da karfe wajen yi wa al’umma aiki? Mu ta yaya talakawa za mu gane da gaske suke yi, tunda suna dambarwa da junansu, sai ka ce a jam’iyyar PDP?
Siyasa na bukatar mutane na kwarai, saboda da ita ake yin mulki, yanzu ta zama wulakantacciyar sana’a, duk wani mugu sai ya ce shi dan siyasa ne, ya yi ta raba kudi a zabe shi, sai abin da hali ya yi, Allah ya sa mu gane, mu canza. Duk wani muhimmin dan takara a PDP ta kewaye shi da wakilanta, su ne ‘yan gaban goshi, na hannun dama. sai an zo kan gaba su karya, don rashin kunya su ci gaba da zama, tare da shi, wasu ma kowa ya san su da PDP, sun rike manyan mukamai a gwamnatin PDP, amma sun ce sun canja sheka, sai sun yi duk illar da aka turasu su yi ga jam’iyyun da ‘yan takarar, sannan su koma inda suka fito, babu kunya, babu tsoron Allah. Hadarin munafuki ya fi na makiyi, ko a Lahira wutar munafukai ba karama ba ce.
Lallai mu lura da Hidisin fiyayyen halitta, kan yadda ya siffanta mana alamomin munafuki uku , wadanda suka hada da: 1-Idan aka ba shi amana ya yi yaudara. 2-Idan ya yi magana ya yi karya. 3-Idan ya yi alkawari ya ki cikawa. Duk wani dan Najeriya mai hankali yasan yadda sashen shari’a da na zartarwa da na dokoki suka lallace, suka sukurkuce, hukumar zabe da jami’an tsaro da dimokuradiyya kanta duk sun zama akwai ya babu. Duk wadanda aka zada da masu hankoron a zabe su, saboda lalacewar al’amarin illa kalilan, da abin da ba a rasa ba, su ma kusan sun bata a yamma, inda rafkanuwar da masu mulki suke yi idan ka ce, ‘subhanallah,’ to, ka zama makiyi, babu maganar gyarawa ko a jawo wani daga bayansa, shi ya koma baya. Ala ayyi halin maganar mulki da shugabanci magana ce ta adalci akan kowa da kowa.
Kowa yasa mulki shi ne karshen karfi na yin gyara ko barna, saboda haka bai kamata a danka mulki a hannun mabarnaci ba. Duk wata amanarmu, ya kamata mu nema mata ahalin da ya dace da ita, musamman amanar rayukanmu da lafiyarmu da dukiyarmu da mutuncinmu da addininmu. Kada mu zo duniya a banza, mu rayu a banza, mu mutu a banza. Babu abin da Allah zai canza mana sai mun canza, mun daina saba wa Allah. karshen halaka, mutum ya yarda, idan ya saba wa Allah sai Allah ya biya masa bukata, har a rika fifita wanin Allah, wa’iyazubillah!
Shin masu fatan mulki ya dawo Arewa wane tanadi suka yi wa hakan? Idan mulki ko Shugabancin Najeriya ya dawo Arewa me suke son cimmawa, ko kuwa kawai muna son mulki a sunan a ce wane dan Arewa shi ne, shugaban kasa ga shi tun kuna fada da junanku, alhali kuma babu wani abu da zai iya kullawa. Idan aka cika gwamnatin da masu bambacin ra’ayi, ina ganin za a iya komawa gidan jiya!
Na farko dai, ‘tun ran gini tun ran zane,’ wadanda suka ginamu akan kabilanci sun yi kuskure. Shi yasa aka wayi gari babu wani da yake batun Najeriya a siyasance, dan Kudu fatansa dan Kudu ko da kuwa babu wani abu da za a tsinana wa mazabarsa. Haka shi ma dan Arewa, ai bincike ya nuna cewa, da dama daga cikin mutanen Kudu maso Kudu suna cikin mawuyacin halin rashin aikin yi da rashin karatu, ga satar mutane ta yi yawa duk kuwa da cewa sitiyarin da ke jan Najeriya dan garinsu ke tuka shi, kowa yasan irin kashe-kashen da ake yi a kasa idan ba haka ba, ku duba irin abuhuwan da suke faru a Arewa maso Gabashin kasar da sauran yankunan Arewa. Kuma irin abubuwan da ke faruwa yanzu a mulkin Jonathan, duk dan takarar da yake son gyara, ya kamata ku zo a hada gwiwa domin kawo gyara a kasa.
Uwar jam’iyyar APC ya kamata ki sulhunta wadancan mutane da ma sauransu. Duk mawadata musamman wadanda suka mallaki rijiyoyin mai da kamfanoni sadarwa da bankuna da masana’antu, su yi kyakkyawan amfani da wannan dama su zuba jarinsu a yunkurinmu na hada kan kungiyoyin da ba na siyasa ba, wadanda ba su da alaka da gwamnati. Su yi mana taimakon gaggawa, tunda har yanzu muna da sauran lokaci wajen magance yunwa da cututtuka, domin rage zafin kiyayyar da ke tsakanin masu mulki da talakawa. Komai girman matsala Allah ya tanadi yadda za a maganceta cikin ruwan sanyi, har ma da yadda za a kauce mata baki daya. Idan an ki sai a yi ta shiga halaka. Fatan mu dai Allah ya tsaremu.
Za a iya tuntubar Makera ta wadannan lambobin waya: 07033882307,08188742103.