Jam’iyyar APC ko PDP: Wace ce ba wace ce ba?
A makonnin baya, Jam’iyyar APC ta samu karin daraja, inda ta bar ‘kasuwar nama’ ta koma cin kasuwa a ‘Eagle Skuare.’ A yanzu ta zama mai yin kafada-da-kafada da Jam’iyyar PDP, domin kuwa ta kwace mata gwamnoni biyar ringis.Idan ba ku gane ba, ‘kasuwar nama’ dai wuri ne da ake yanka shanu da sauran dabbobi […]
A makonnin baya, Jam’iyyar APC ta samu karin daraja, inda ta bar ‘kasuwar nama’ ta koma cin kasuwa a ‘Eagle Skuare.’ A yanzu ta zama mai yin kafada-da-kafada da Jam’iyyar PDP, domin kuwa ta kwace mata gwamnoni biyar ringis.
Idan ba ku gane ba, ‘kasuwar nama’ dai wuri ne da ake yanka shanu da sauran dabbobi domin sayarwa. ‘Eagle Skuare’ kuwa dandali ne a Abuja, inda masu mulkin Najeriya (kafin su tsorata) suke shirya tarukansu na siyasa.
A lokacin da dan siyasa ya gawurta, har ta kai cewa yana shirya taruka a ‘Eagle Skuare,’ to babu shakka hakan na nuna cewa ya kawo karfi ke nan, wanda Hausawa kan ce, ya fi ka grime ni. Wannan kuma na nuna cewa lallai dan siyasar nan na gab da shiga gidan gwamnati. Wannan dalili ne ma ya sanya a makon na jiya, cikin PDP ya duri ruwa, ta rikice, tana ta kwarmato, tun daga yankin ’yan Boko Haram har zuwa yankin ’yan tsageran Bayelsa.
Ta bangarena, tun a 2004 ne na fara nuna kwarmato game da cin kashin PDP, domin kuwa tun a lokacin na fahimta da alkiblarta. Jam’iya ce da take cike da kwamacala da jagwalgwalo da dagwalo mai munin wari. Tun lokacin nan na fahimci haka, har zuwa makon na jiya, inda aka ingiza wani daga cikin dagwalon PDP zuwa APC.
Bari mu bi dalla-dalla, mu ga yadda al’amarin jam’iyyun yake: Ita dai PDP, jam’iyya ce mai taurin kai, mai cike da ha’inci da rashawa, sannan kuma ga ta ba ta tsinana wa talakan Najeriya komai. Haka kuma, kamar yadda tsofaffin membobin nata da suka canja sheka suka nuna, sun ce shugabannin PDP sun jahilci yadda ake tafiyar da jam’iyya, ba su da masaniyar cewa jam’iyyar siyasa ba kungiyar sharholiya ba ce.
Kamar yadda na fada a wani rubutu da na yi a farkon shekarar nan: “Masu laifi a Najeriya ba a PDP kadai suke ba, kawai dai ita ta zama kamar tambarin lalacewar Najeriya ne, musamman saboda ita ce ta yi kaka-gida a kan mulki, wadda ta fi kowa lalata al’amura. Amma idan aka lura, sauran jam’iyyun da suke mulkin wasu jihohi a Najeriya tun shekaru 14 da suka gabata, ai ba wankakku ba ne.”
A yanzu ma zan sake nanatawa, matsalarmu ba kawai ta tsaya ga PDP ba ne, kalubalen na dukkan ’yan sisayar Najeriya ne.
Ita APC tana kokari ne ta kawar da Goodluck Jonathan da jam’iyyarsa ta PDP daga kan mulki a 2015. Wannan yunkuri ne na halal kuma wanda ya dace amma abin tambayar shi ne, wane sauyi take shirin kawowa fiye da na PDP? Ko kuwa tana nufin ita ma wata PDPin ce mai dauke da sabuwar fuska?
Idan za mu yi wa APC adalci, ta bayyana kudurorinta, cewa za ta mayar da hankali wajen bunkasa al’amuran noma, samar da ayyukan yi, samar da ilimi kyauta ga al’umma, samar da wadatattar wutar lantarki, samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya, magance matsalar talauci da taka wa cin hanci da rashawa birki, samar da yanayin bunkasa gine-gine, bunkasa masana’antu da kuma kere-kere.
Duk da cewa kowa zai ji dadin jin wadannan kudurori amma a zahiri batun bai da wani muhimmanci, domin kuwa ’yan Najeriya sun dade suna jin irin wadannan bayanan. Abin da suke bukata shi ne, aiki na zahiri ba surutu ba. Hatta sojoji, idan sun karbi mulki, da irin wadannan surutan suke fakewa, kafin su bayyanar da nasu makircin.
Abin tambaya a nan shi ne, ta yaya APC za ta bambanta kanta da bahallatsar da PDP ta dade tana tafkawa?
Amsa ita ce: da’a: da’a, ita ce abin nema ga dukkan wani dan siyasar da zai iya kawo canji mai amfani ga al’umma.
A wani zancen kuma, duk yadda na ki jinin PDP, idan har APC ta gaza nuna da’a mai kyau, to duk zancen daya ne da PDP. Domin kuwa duk mutumin da ya biye wa mahaukaci, suka yi kokowa da shi, to babu yadda zai bambanta kansa da hauka.
Kuma ni a yadda nake kallon al’amura, abin da APC take yi ke nan, wato fada da mahaukaciya – PDP. Ba ma haka ba, a hakikanin gaskiya, abin da take yi ma ya fi wannan muni. Na farko dai, ta yi zagaye tana ziyartar Olusegun Obasanjo da Ibrahim Babangida, wai da nufin neman ‘tubarrakinsu.’ Abu na biyu kuma shi ne, yadda APC ta fake da rashin jituwar da ke faruwa tsakanin ’yan PDP, ta karfafa wa wasu ’ya’yanta suka shigo cikinta.
Dukkan wadannan abubuwan da APC ta yi, babu wanda ya halatta kuma babu wanda ya zama wani abin karfafa gwiwa. Wani abin lura kuma shi ne, masu tafiyar da tsare-tsaren jam’iyyar da mafi yawa daga hamshakanta, duk daga PDP suke kuma salon PDP suke gudanarwa a al’amuransu.
Za mu ci gaba