Jam’iyyar APC kulob ce za ta iya darewa a kowane lokaci – Mamuda Kuit

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Jigawa Alhaji Salisu Mamuda Kuit ya shawarci shugabannin bangarorin Jam’iyyar PDP na kasa Sanata Ali Modu Sheriff da Sanata Ahmed Makarfi da sauran magoya bayansu su ajiye makamansu su tsaya su hada kai su wajen taimaka wa jam’iyyar ta inganta.Alhaji Salisu Mamuda ya ba da tabbacin cewa muddin suka hada […]

Jam’iyyar APC kulob ce za ta iya darewa a kowane lokaci – Mamuda Kuit
Jam’iyyar APC kulob ce za ta iya darewa a kowane lokaci – Mamuda Kuit

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Jigawa Alhaji Salisu Mamuda Kuit ya shawarci shugabannin bangarorin Jam’iyyar PDP na kasa Sanata Ali Modu Sheriff da Sanata Ahmed Makarfi da sauran magoya bayansu su ajiye makamansu su tsaya su hada kai su wajen taimaka wa jam’iyyar ta inganta.
Alhaji Salisu Mamuda ya ba da tabbacin cewa muddin suka hada kansu babu shakka za su karbe mulki daga hannun gwamnatin APC, inda ya ce sanin kowane Jam’iyyar APC kamar kulob ce kuma wani tsari ne na kasuwancin hannun jari na mutum biyu ta yadda daya daga cikinsu yana cire hannun jarinsa tafiyar za ta wargaje.
Alhaji Mamuda Kuit ya ce ko shakka babu za su karbe ragamar shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa domin kowa ya  fahimci inda gwamnatin APC ta karkata akalarta tun ba a je ko’ina ba.
Ya ce rikicin da ke faruwa a cikin jam’iyyarsu ta PDP a tsakanin Sanata Ahmed Makarfi da Sanata Sheriff alheri ne, kuma yanzu kotu ta kawo karshensa nan ba da dadewa ba za su gudanar da zaben sababbin shugabannin jam’iyyar na kasa tunda a baya an rigaya an yi na unguwanni da kananan hukumomi da jihohi da shiyya-shiyya abin da ya rage na kasa ne da waccan rigimar ta hana.
Alhaji Mamuda Kuit ya roki Sanata Sheriff da Sanata Makarfi su yi hada kansu su bai wa marada kunya wajen hada kan ’ya’yan jam’iyyar don ganin an samu kawo ci gaba.
Ya ce Jam’iyyar PDP, jam’iyyace ta ’yan Najeriya da babu ruwanta da maganar bangare ko sashin da mutum ya fito balle maganar kabilanci, “ita jamiyya ce da ta rungumi kowa a matsayin danta, sabanin mulkin da APC ke yi yanzu, mulkin kama-karya da danniya da fin karfi da nuna bambanci,” inji shi.
Ya nuna damuwarsa game da halin ko in kula da gwamnatin ta sanya manoma a ciki na rashin wadata su da takin zamani a daminar bana sabanin lokacin da gwamnatinsu da ta rika bai wa manoma taki kamar a banza.