Jamiyyar APC Reshen Jihar Edo Ta Yaba wa Wakilanta
Sakataren jam’iyyar APC, reshen Jhar Edo, Comrade Gogwin Erhahon ya bayyana farin ciki tare da yabo game da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyya a makon da ya gabata, inda ya ce mun samu wannan nasara ne saboda hadin kai da ra’ayin magoya bayan wannan jam’iyyar a matsayin ’yan kasa masu kishi […]
Sakataren jam’iyyar APC, reshen Jhar Edo, Comrade Gogwin Erhahon ya bayyana farin ciki tare da yabo game da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyya a makon da ya gabata, inda ya ce mun samu wannan nasara ne saboda hadin kai da ra’ayin magoya bayan wannan jam’iyyar a matsayin ’yan kasa masu kishi da tunani na kwarai.
Ya ce wadanda ba su samu nasara ba sun karbi hakan, to zai zamar musu mafita ku sani cewa za a saka muku daidai da yadda kuka sauya, abin ya je daidai a lokuta da dama kun zama masu nasara na zaman lafiya da hadin kai ga wannan jam’iyyar.
Kuma wakilai da suka yi zaben fidda gwani na dan takaran shugaban kasa a legos makon jiya sun zabi mutumin kwarai da ’yan Najeriya suka fi so, kuma suka yarda da shi ya shugabancesu, babu wani bambanci, domin ceto al’umma daga halin ni ’ya su da gwamnatin PDP ta jefa su a ciki. Don haka jam’iyyar APC ta bukaci mutum mai imani, ta zabi Janar Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa ba irin mutumin da za a samu matsala a wajen zaben shi ba.