Jam’iyyar APC ta dinke barakarta a Jihar Borno

Jam’iyyar APC a Jihar Borno ta dinke barakar da ta kunno kai a tsakanin ’ya’yanta kusan shekara daya da ta gabata, inda aka samu daidaito a tsakanin Gwamna Kashim Shettima da tsohon Gwamna Sanata Ali Sheriff, bayan da Mutawalli Kashim Ibrahim Imam ya shiga tsakaninsu.Gwamna Kashim Settima ya fada wa manema labarai a wani taro […]

Jam’iyyar APC ta dinke barakarta a Jihar Borno
Jam’iyyar APC ta dinke barakarta a Jihar Borno

Jam’iyyar APC a Jihar Borno ta dinke barakar da ta kunno kai a tsakanin ’ya’yanta kusan shekara daya da ta gabata, inda aka samu daidaito a tsakanin Gwamna Kashim Shettima da tsohon Gwamna Sanata Ali Sheriff, bayan da Mutawalli Kashim Ibrahim Imam ya shiga tsakaninsu.
Gwamna Kashim Settima ya fada wa manema labarai a wani taro cewa “A yau mun dinke duk wata barakar da ta kunno kai a tsakaninmu mun kuma amince za mu yi aiki tare don kai jam’iyyarmu ga tudun mun tsira, mun kuma amince kowa ya tsaya a matsayinsa, sannan mun amince da samun daidaito a tsakanin ’yan takarar da suka amince da yin sulhu a tsakaninsu, don haka ina kira ga magoya bayan wannan jam’iyya tamu da al’umman jiha su ba mu cikakken hadin kai da goyon baya don kai jam’iyyar ga tudun mun tsira.”
Shi ko Sanata Ali Sheriff wanda har ila yau shi ne ubangidan siyasar Gwamna Shettima ya ce, “Da ma sha’anin siysa ana samun rashin fahimta ko rashin amincewa sakamakon bambancin ra’ayi a tsakanin ’ya’yan jam’iyya. To amma yanzu komai ya zo karshe, mun daidaita mun fahimci juna za mu hada hannu mu yi aiki tare. A yau Gwamna Kashim ne jagoran jam’iyya, ina so ku sani cewa ba ina jayya ne da kasancewarsa jagoran jam’iyya ba, kuma mun amince kowa ya tsaya a matsayinsa, saboda haka na gode wa Mutawalli Kashim Ibrahim Imam kan tsayin dakarsa da hana idonsa barci don ganin ya hada hancin wannan tafiya.”
Mutawalli Kashim Iman ya ce “Sabanin ra’ayin siyasa ba sabon abu ba ne, to amma bai kamata ya yi tsanani ba. Saninku ne muna fama da matsalar rashin tsaro a jiharmu, yau a kashe wannan, gobe wancan, wannan ne babbar matsalar da ta kamata a fi damuwa a kai ba rashin fashimtar siyasa ba. Kuma muna rokon ’ya’yan jam’iyya su yi kokarin gina ta yadda al’ummar jihar za su ci moriyar mulkin dimokuradiyya.”