Jam’iyyar APC ta kasa cika wa al’ummar Keffi alkawuran da ta yi musu
Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa wanda a yanzu ya fito takarar shugaban jam’iyyar a karamar Hukumar Keffi, Alhaji Aliyu Muhammed Babayo ya ce har yanzu Jam’iyyar APC a karamar hukumar ta gaza cika alkawurran da ta yi wa al’ummar Keffi a lokacin yakin neman zabe. Alhaji Aliyu Babayo ya bayyana haka ne […]
Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa wanda a yanzu ya fito takarar shugaban jam’iyyar a karamar Hukumar Keffi, Alhaji Aliyu Muhammed Babayo ya ce har yanzu Jam’iyyar APC a karamar hukumar ta gaza cika alkawurran da ta yi wa al’ummar Keffi a lokacin yakin neman zabe.
Alhaji Aliyu Babayo ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a garin Keffi, inda ya ce al’ummar karamar hukumar, musamman matasa na fuskantar mawuyacin hali a yanzu sakamakon gazawar Jam’iyyar APC wajen samar musu da ribar dimokuradiyya, inda ya ce a yanzu matasan suna kukan rashin aiki kuma babu wani tallafi daga gwamnatin APC a karamar hukumar.
Ya ce Jam’iyyar APC ta yi wasi da bukatun al’ummar karamar hukumar da suka hada da rashin isassun asibitoci da ruwan sha da hanyoyin karkara da sauransu, inda ya ce duk da cewa shugababan karamar hukumar Alhaji Muhammed Dikko kanensa ne kuma ya dade yana ba shi shawara a kan yadda zai gudanar da shugabanci nagari don ci gaban karamar hukumar amma ba ya aiki da shawarwarin.
Ya bukaci al’ummar karamar hukumar su tabbatar sun kawar da Jam’iyyar APC a zabubbuka masu zuwa a karamar hukumar domin samun canji mai ma’ana.
Sai ya musanta jita-jitar da wasu ke yadawa cewa PDP ba ta da karfi a karamar hukumar inda ya ce har yanzu ita ce jam’iyya mafi yawan jama’a, kuma ya ce faduwarta a zaben baya kuskuri ne daga wasu mambobin jam’iyyar.
Alhaji Aliyu Babayo ya ce ya yanke shawarar neman shugabancin ne don dawo da martabar PDP a karamar hukumar da jihar baki daya. Ya ce rashin hadin kai da kyashi a tsakanin wasu ’ya’yan PDP ne suka jawo faduwarta a zabubbukan da suka gabata inda ya ce da zarar ya samu nasara zai samar da hanyoyin sulhu a tsakanin mambobin jam’iyyar a kowane mataki don kwato mulki daga hannun APC a karamar hukumar da jihar.