Jam’iyyar APC ta kori Sanata danjuma Goje

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Gombe Barista Muhammad Magaji Doho, ya bayyana korar tsohon Gwamnan Jihar Sanata Muhammad danjuma Goje da wasu magoya bayanta daga jam’iyyar. Barista Magaji Doho ya bayyana korar toshon Gwamnan ne a wani taron manema labarai da ya kira a ranar Talata a Gombe.Barista Magaji Doho, ya ce sun kori Sanata […]

Jam’iyyar APC ta kori Sanata danjuma Goje
Jam’iyyar APC ta kori Sanata danjuma Goje

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Gombe Barista Muhammad Magaji Doho, ya bayyana korar tsohon Gwamnan Jihar Sanata Muhammad danjuma Goje da wasu magoya bayanta daga jam’iyyar.

Barista Magaji Doho ya bayyana korar toshon Gwamnan ne a wani taron manema labarai da ya kira a ranar Talata a Gombe.
Barista Magaji Doho, ya ce sun kori Sanata danjuma Goje da wasu ’ya’yan jam’iyyar ne saboda bincikensu ya gano cewa suna yi wa jam’iyyar kafar ungulu kuma su ne makasudin jawo wa jam’iyyar matsalar da ta kai ta ga faduwa a zaben Gwamnan Jihar.
Sanata danjuma Goje dai shi ne Sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.
Shugaban jam’iyyar ya kuma ce dade da gano cewa duk wata matsala da jam’iyyar ke fuskanta a jihar ba wani ne yake jawo su ba illa Sanata danjuma Goje, kuma ya ce a lokacin da Buhari ya zo Gombe don yakin neman zabe kamata ya yi a ce kowa nasa ne amma Sanata Goje, ya yi babakere ya hana dan takarar Gwamnan kusanta Buhari shi kuma ya rika cusa kansa.
“Ko a lokacin da Buhari ya je fada don gaida Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, Sanata Goje ya sa Buhari ya sauka daga kan mota shi ya hau sama, to shin a lokacin tallar dan takarar Gwamna ake yi ko tallar Sanata,” inji Doho.
Ya ce haka a lokacin zuwan Buhari garin Gombe karo na biyu da ya je Akko, Sanata Goje ya sake kusantar Buhari ya hana dan takarar Gwamnan ya kusance shi domin ko mota daya Goje bai bar dan takarar ya shiga da Buhari ba, nan ma Goje ne ya shiga mota daya da Buhari, kuma irin haka ne ya sa yanzu a Gombe APC ta rabu gida biyu.
Barista Magaji Doho, ya ce sun gane cewa ba ya ga ungulu da kan zabo da ya rika yi wa jam’iyyar kuma ba ya mutunta ta ne ya sa suka sallame shi daga APC.
Sauran wadanda aka sallama tare da Goje sun hada da danjuma Babayo Sakataren Tsare-Tsare na jam’iyyar da Sallau Kachalla Sakatare da Umar Muhammad Shaiffudeen da Hajiya Lumbi Mataimakiyar Shugabar Mata da Hajiya Larai Mataimakiyar Sakataren Shiyya da Walin
Awak Mataimakin Shugaba na Shiyyar Gombe ta Kudu da Magret Shugabar Mata ta Gombe ta Kudu da sauransu.
Sai ya ce kwamiti zai ci gaba da bincike don gano duk mai son kawo wa jam’iyyar cikas don su
kore shi su yi wa jam’iyyar gyara don ta tsaya da kafafunta.
Ya ce sun dakatar da gudanar d aikace-aikacen jam’iyyar a sakatariyarta da ke kan hanyar Bauchi sun koma karamar sakatariyar jam’iyyar na karamar hukuma da ke kusa da barikin soji.