Jam’iyyar APC ta kwana da sanin cewa ’yan Nijeriya na fama da yunwa — Mathew Kukah

Ya kamata jam’iyya mai mulki ta yi duk abin da zai yiwu domin rage raɗaɗin da talakawa ke fuskanta.

Jam’iyyar APC ta kwana da sanin cewa ’yan Nijeriya na fama da yunwa — Mathew Kukah

Bishop Mathew Hassan Kukah

Babban limamin mabiya ɗarikar Katolika da ke Sakkwato, Bishop Mathew Hassan Kukah, ya buƙaci shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar da su kwana da sanin cewa ’yan Nijeriya na fama da yunwa da ƙuncin rayuwa a dalilin tsadar farashin man fetur a halin yanzu.

Yayin wani jawabi da ya gabatar a ranar Juma’a a Abuja, Bishop Kukah ya buƙaci jagororin jam’iyyar mai mulki a ƙasar da su yi duk mai yiwuwa domin rage raɗaɗin da talakawa ke fuskanta.

Ana iya tuna cewa a ranar Talata ce Kamfanin Mai na NNPCL na Najeriya ya ƙara farashin lita guda na man fetur zuwa naira 855 daga naira 568.

Su kuma ’yan kasuwa na sayar da lita guda tsakanin naira 930 zuwa 1,200 a gidajen mai daban-daban a faɗin Najeriya.

Amma da yake isar da saƙon fatan alheri a yayin taron jam’iyyar APC, Kukah ya ce, “Mu ‘yan Najeriya muna jin yunwa. A nemo hanyar rage farashin man fetur ɗin.

“Sai dai idan ba a kafa dimokuraɗiyya a kan ingantaccen tushe ba, za mu yi gini a kan yashi. Na damu da ingancin dimokuraɗiyya a Najeriya. Ya kamata mu gyara matsalar dimokradiyya a Najeriya.”

Shugabannin jam’iyyar APC da suka halarci taron da ya gudana a otal ɗin Continental da ke Abuja, sun haɗa da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje; Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wanda mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya wakilta; da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.

Sauran sun haɗa da shugaban Ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma; Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa; ministoci; shuwagabannin APC na jihohin da sauransu.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos