Jam’iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomin Jihar Kano

Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kano ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 44 da na kansiloli 848 da ke fadin jihar, a zaben kananan hukumomin da aka gudana a ranar Asabar da ta gabata. Da farko dai zaben ya fuskanci matsalolin da suka hada da jinkirin kai kayan zabe a rumfunan zabe tare da […]

Jam’iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomin Jihar Kano
Jam’iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomin Jihar Kano

Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kano ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 44 da na kansiloli 848 da ke fadin jihar, a zaben kananan hukumomin da aka gudana a ranar Asabar da ta gabata.
Da farko dai zaben ya fuskanci matsalolin da suka hada da jinkirin kai kayan zabe a rumfunan zabe tare da ’yan tashe-tashen hankula da suka hada da kame kayan aikin zabe da matasa suka yi a karamar Hukumar Kunchi.
A karamar Hukumar Kura, kuwa matasan ne suka lalata kayan aikin zabe, kafin a sake kai wasu kayan aikin. Hakan baya rasa nasaba da zargi tare da bukatar yin nasara a tsakanin mabiya jami’iyyun APC da PDP a jihar.
A karamar Hukumar kiru kuwa ’yan sanda ne suka harbi mutum bakwai, inda mace daya daga cikinsu ta rasu nan take. Mutanen garin sun ce an harbe su ne saboda sun ki yarda a hada baki da ’yan sanda da tsohon shugaban majalisar jihar, Gambo Sallau wajen kautar da kayan zaben don yin magudi. Sai dai ’yan sanda sun ce sun yi harbin ne don kwatar kansu daga gungun matasan da suka far musu.
Tsohon Gwamnan Jihar, Malam Ibrahim Shekarau ya ce ba a yi zabe ba, don haka kotu za su je don su kai hujjojinsu, saboda suna da hujjoji a kan hakan.
Shi kuwa Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya ce sakamakon zaben ya nuna gamsuwar mutanen Kano da salon mulkinsu a jihar, yana mai cewa suna sa ran samun gagarumar nasarar da ta fi wanna a zabubbuka na gaba.