Jam’iyyar APC ta lashe zaben Sanatan Imo ta Arewa

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta bayyana Mista Ben Uwajumogu na Jam’iyyar APCa matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na Sanatan Imo ta Arewa da aka gudanar a karshen makon jiya.A cewar Hukumar INEC, Mista Uwajumogu ya samu kuri’a dubu 56 da 76 inda ya doke abokin takararsa na Jam’iyyar PDP Mista Athan Achonu, […]

Jam’iyyar APC ta lashe zaben Sanatan Imo ta Arewa
Jam’iyyar APC ta lashe zaben Sanatan Imo ta Arewa

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta bayyana Mista Ben Uwajumogu na Jam’iyyar APCa matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na Sanatan Imo ta Arewa da aka gudanar a karshen makon jiya.
A cewar Hukumar INEC, Mista Uwajumogu ya samu kuri’a dubu 56 da 76 inda ya doke abokin takararsa na Jam’iyyar PDP Mista Athan Achonu, wanda ya samu kuri’a dubu 43 da 815.
Babban Jami’in Tattara Sakamakon Zabe na Gundumar Imo ta Arewa, Mista Arinze Agbogu, wanda ya bayyana sakamakon zaben a ranar Juma’ar da ta gabata ya ce, sakamakon ya samu ne ta hanyar tattara kuri’un da aka kada a ranakun 23 da 28 ga watan Yulin bana.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya da ya ruwaito labarin ya ce, Mista Uwajumogu, ya samu kuri’a dubu 48 da 921 a ranar 23 ga Yuli, yayin da Mista Achonu na PDP ya samu kuri’a dubu 40 da 142 lamarin da ya sa Hukumar INEC ta bayyana cewa zaben cike-gurbin bai kammalu ba.
Mista Agbogu ya ce alkaluman da suke gabansa sun nuna Mista Uwajumogu ya samu kuri’a mafi rinjaye don haka shi ne ya lashe zaben Sanatan Imo ta Arewa.
Har wa yau Hukumar INEC ta bayyana Nkenna Nzeruo na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar jihar daga mazabar Oru ta Gabas, yayin da Collins Chiji shi ma na APC ya lashe zaben mazabar dan majalisar jihar na Isiala Mbano.
An dakatar da zaben mazabun biyu ne sakamakon rahotannin tashin hankali a wasu yankuna biyu a zaben na 23 ga Yuli.
 Mista Uwajumogu ya shaida wa manema labara cikakken jin dadinsa kan lashe zaben tare da mika godiya ga Gwamnan Jihar Rochas Okorocha wanda ya ce gadon bayansa ya hau ya kai ga nasara.