Jam’iyyar APC ta sake darewa a Jihar Zamfara
Marafa ya karyata zargin da ake cewa bangarensa ne ya kai Jam’iyyar APC kotu a 2019.
Jigon Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya sanar da sake farfado da bangarensa, a yayin da rikicin da ya barke a jam’iyyar a jihar ke kara ruruwa.
Idan ba a manta ba, rikicin da ya barke tsakanin Sanata Marafa da tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari da ya kai ga rabewar jam’iyyar a shekarar 2018 ne ya sa aka kwace dukkan kujerun da jam’iyyar ta samu a zaben 2019 ciki har da ta Gwamna, aka ba wa Jam’iyyar PDP, bayan Kotun Koli ta tabbatar da karar da Marafa ya shigar yana kalubalantar zaben fid-da-gwanin da ya samar da ’yan takarar jam’iyyar.
- Yadda ’yan mata suka koma fasakwaurin shinkafa a Kudu
- Karin kuɗin ruwan da CBN ke yi na illata masana’antu da jawo rasa aiki — Ɗangote
A lokacin da Ministan Tsaro na yanzu, Bello Matawalle ya zama Gwamnan Jihar bayan hukuncin Kotun Koli, ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC, inda ya sha kaye a zaben Gwamna na 2023, sakamakon rashin warware rikicin cikin gida na jam’iyyar.
Da yake jawabi ga manema labarai a Kaduna, a yayin wani taro da daruruwan magoya bayansa da suka fito daga Jihar Zamfara, Sanata Marafa ya ce, an samu bangarori biyu a Jam’iyyar APC tun lokacin da rikicin ya barke a gwamnatin Yari, kuma hakan ya ci gaba a zamanin Matawalle.
A cewarsa, rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a cikin shekara shida da suka gabata ya samo asali ne daga muradun manyan jiga-jigan siyasa a jihar.
Sanatan da ya wakilci Zamfara ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta 7 da ta 8, ya sanar da sake dawowar bangarensa domin nuna rashin amincewarsa da rashin halartar taron jam’iyyar da aka yi kwanan nan a jihar.
Ya aminta da cewa, rikicin ya sa jam’iyya mai mulki ta sha kayi a manyan zabuka a jihar, in ban da na Shugaban Kasa, inda shi ya yi aiki a matsayin kodineta na kungiyar yakin neman zaben Tinubu da Shettima.
Da yake nisanta kansa da rikicin da ya barke a jihar, ya karyata zargin da ake cewa bangarensa ne ya kai Jam’iyyar APC kotu a 2019.
Ya bayyana cewa, jam’iyyar a Zamfara ta gudanar da zaben fid-da-gwani ba bisa ka’ida ba, inda ya garzaya kotu domin neman halaccin gudanar da wannan zabe.
“Za mu sake dawo da bangarenmu, wanda muka rushe ya koma Yari domin shi ne bangaren da APC ta amince da shi a wancan lokacin.
“Tunda mun yarda mun taru, babu bukatar mu yaudari kanmu ta hanyar wasu kungiyoyi.
“Abin da Matawalle ya yi ke nan a matsayinsa na shugaban jam’iyyar tun yana gwamna.
“Daga yau na umurci mabiyana da su sake farfado da bangarenmu tun daga rumfunan zabe har zuwa jiha domin abin da shugabannin Jam’iyyar APC ke so ke nan.
“Koyaushe akwai tasiri a cikin duk abin da kuke yi. Mun kasance a kan wannan hanya a baya, kuma mun san hanyar,” inji shi.