Jam’iyyar APC ta yi babban kamu a Kano

An yi bikin karbar tsohon dan Majalisar Wakilai ta Tarayya na mazabar Bichi, Hon. Lawan Shehu a yamacin Asabar din da ta gabata, inda Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kasance babban bako a wajen bikin tare da sauran kusoshin gwamnatin jihar. A jawabinsa, Gwamna Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta na […]

Jam’iyyar APC ta yi babban kamu a Kano

An yi bikin karbar tsohon dan Majalisar Wakilai ta Tarayya na mazabar Bichi, Hon. Lawan Shehu a yamacin Asabar din da ta gabata, inda Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kasance babban bako a wajen bikin tare da sauran kusoshin gwamnatin jihar.

A jawabinsa, Gwamna Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta na da kyawawan manufofi, sannan ita ce kadai jam’iyyar da ta yi tanade-tanade masu amfani ga al’umar Najeriya ba tare da nuna wani bambanci ba saboda ciyar da kasa gaba.

Sannan ya nunar da cewa gwamnatin APC bisa jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari tana daukar matakai ingantattu domin ganin kasar nan ta sauya ta kowane fanni, don haka a cewar gwamnan, jam’iyyar APC za ta ci gaba da jajircewa domin ceto kasar nan daga mawuyacin halin da take ciki domin samar da rayuwa ingantacciya ga ‘yan Najeriya.

A karshe, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana Hon. Lawan Shehu a matsayin dan siyasa wanda yake da kyawawan manufofi na kawo ci gaba ga al’uma musamman ganin irin yadda yake tafiyar da harkokinsa na siyasa da mu’amala da mutane ba tare da nuna kyamar kowa ba.

A nasa tsokacin, Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas ya ce a kullum jam’iyyar ta na samun magoya baya tare da karbar mutane masu kaifin hankali cikin ta wanda hakan ya nunar da cewa jam’iyyar tana cike da alheri idan aka dubi yawan al’umar da suke kwarara cikinta a kowane bangare na fadin kasar nan, inda kuma ya sanar da cewa Najeiya za ta sami managarcin cigaba a karkashin APC.

Dangane da canjin shekar da ya yi zuwa APC kuwa, Hon. Lawan Shehu ya yi godiya ga Ubangiji bisa yadda aka gudanar da wannan taro cikin nasara da farin ciki bisa karbar sa cikin jam’iyyar daga ta adawa PDP, inda ya sanar da cewa kyawawan manufofin jam’iyyar ne suka sanya shi yanke shawarar tsunduma cikinta domin a hadu wajen ciyar da kasa gaba ta kowane fanni.