Jam’iyyar APC ta yi tir da sake nada kantomomi a kananan hukumomin Jihar Bauchi
Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ta nuna rashin gamsuwa kan sake nada shugabannin kwamitin rikon kwarya da za su ci gaba da gudanar mulkin kananan hukumomin jihar 20 ba tare da aiwatar da zabe ba.Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Bauchi Alhaji Uba Ahmed Nana ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya kira […]
Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ta nuna rashin gamsuwa kan sake nada shugabannin kwamitin rikon kwarya da za su ci gaba da gudanar mulkin kananan hukumomin jihar 20 ba tare da aiwatar da zabe ba.
Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Bauchi Alhaji Uba Ahmed Nana ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya kira a ofishinsa don nuna rashin amincewar jam’iyyar da nuna bacin ransu kan rashin samar da kudi ga hukumar zabe ta jihar don gudanar da zaben.
Ya ce nada kantomomin ya saba wa dokar zabe ta bakwai a kundin tsarin mulkin Najeriya.
Alhaji Uba Nana ya zargi ’yan Majalisar Dokokin Jihar da bari a yi amfani da su wajen sake nadan sababbin shugabannin rikon, alhali suna cikin wadanda ke cin gajiyar zabe a karkashin dimokuradiyya.
Ya ce bai dace ’yan majalisar su zama ’yan amshin shatan Gwamna suna bari ana yin nadi a madadin gudanar da ingantaccen zabe da zai ba jama’a damar zaben shugabannin da suke so.
Alhaji Uba Nana ya ja hankalin gwamnatin jihar ta hanzarta biyan kudin fansho da garatutin ma’aikatan da suka bar aiki da tsawon lokaci ba su samu kudinsu na sallama ba.
Ya kuma bukaci gwamnatin ta maida hankali wajen gina kananan masana’antu don sama wa matasa guraben aiki don a rage aikata laifuffuka da zaman kashe wando da ke haifar da fitina a tsakanin matasa.