Jam’iyyar APC ta zabi shugabanninta a jihohin Kebbi da Neja da Jigawa
A cikin wannan makon ne Jam’iyyar APC ta gudanar da zabubukan shugabanninta a jihohi da dama na kasar nan.Wakilinmu na Jihar Kebbi Bashir Lawal Zakka ya ce jam’iyyar ta gudanar da zaben ne a karkashin shugaban kwamitin zabe, danduba Mohammed, kuma mutum biyu ne suka fafata a takarar kujerar shugaba wato Alhaji Abubakar Atiku Bunu […]
A cikin wannan makon ne Jam’iyyar APC ta gudanar da zabubukan shugabanninta a jihohi da dama na kasar nan.
Wakilinmu na Jihar Kebbi Bashir Lawal Zakka ya ce jam’iyyar ta gudanar da zaben ne a karkashin shugaban kwamitin zabe, danduba Mohammed, kuma mutum biyu ne suka fafata a takarar kujerar shugaba wato Alhaji Abubakar Atiku Bunu da Lauya Attahiru Maccido.
Sakamakon zaben ya nuna Lauya Maccido ne ya samu nasarar zama shugaba da kuri’a 668, yayin da Alhaji Abubakar Atiku Bunu ya samu kuri’a 598.
Da yawa daga cikin wakilan zaben sun bayyana gamsuwa bisa yadda aka gudanar da zaben ba tare da fuskantar wata matsala ba.
Sabon Shugaban Jam’iyyar APC, Lauya Attahiru Maccido, ya ce zai tafi da kowa da kowa a jam’iyyar ba tare da nuna wani bambanci ba, don haka ya yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar su hada hannu domin ciyar da ita gaba.
Lauya Attahiru Maccido, ya ce Jam’iyyar PDP wacce take mulki tun daga 1999 ta kamu da cutar kanjamau, don haka Jam’iyyar APC ce za ta kafa gwamnati a jihar da kananan hukumomi da Najeriya in Allah Ya yarda.
Daga Minna wakilinmu Muhammad danladi Ibrahim ya ce Jam’iyyar APC ta zabi Injiniya Muhammad Jibril Adamu Imam Gawu daga karamar Hukumar Gurara a matsayin shugabanta na jihar.
Ya ce masu zabe daga gundumomi 274 na kananan hukumomin jihar 25 sun hadu a Kasuwar Duniya da ke Minna inda Barista dalhatu Usman batagarawa ya shugabanci kwamitin zaben da ’yan takara 32 suka fafata a kujeru da dama.
Sabon shugaban Injiniya Muhammad Imam Gawu ya ce yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da amincewa da sakamakonsa da ’yan takara suka yi alama ce ta dattaku da ba za su mance ba.