Jam’iyyar APC za ta kai Gwamna dakingari kotu idan…
Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi ta yi barazanar kai Gwamnan Jihar Alhaji Sa’idu Nasamu dakingari kotu muddin bai sauke shugabannin kananan hukumomi 21 da ke jihar da wa’adinsu zai kare ranar 15/09/2014.Sakataren Watsa Labara na Jam’iyyar Alhaji Sani Dodo ne, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da jam’iyyar ta kira a kan cikar […]
Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi ta yi barazanar kai Gwamnan Jihar Alhaji Sa’idu Nasamu dakingari kotu muddin bai sauke shugabannin kananan hukumomi 21 da ke jihar da wa’adinsu zai kare ranar 15/09/2014.
Sakataren Watsa Labara na Jam’iyyar Alhaji Sani Dodo ne, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da jam’iyyar ta kira a kan cikar wa’adin shugabannin kananan hukumomin.
Alhaji Sani Dodo ya ce APC ta yanke shawara cewa da zaran gwamnatin Jihar Kebbi ta kara wa shugabannin kananan hukumomi koda kwana daya ne a kan shekara biyu da doka ta tanada, za su maka Gwamna dakingari a kotu domin jin dalilin kara musu lokaci.
Sakataren ya ce doka ta tanadi a shirya wani zabe ba tare da nada kantomomin riko ba, kuma jam’iyyarsu ta APC a shirye take domin gudanar da zaben.
Ya jawo hankalin Gwamna dakingari a kan kashe sama da Naira biliyan 17 wajen gina filin jirgin sama, inda ya ce ba ya da amfani ga al’ummar Jihar Kebbi.
Ya ce maimakon kashe wadannan makudan kudi kudi kan gina filin jirgin sama, abin da ya fi alheri a samar wa jama’a sababbin hanyoyin noma na zamani da taki da iri da magungunan noma a kan lokaci ko a gina kamfanonin da za su samar da aiki ga mutane.
“Daga nan Birnin Kebbi zuwa Sakkwato tafiyar kilomita 120 ne, ina amfanin gina filin jirgi a Birnin Kebbi. Idan aka yi amfani da Naira biliyan 10 aka gina kananan kamfanoni na ruwa ko madara ko na robobi ko gyada ko sarrafa shinkafa. Sauran Naira biliyan bakwai sai a kara inganta asibitoci da magungunna da isassun likitoci da kayan aiki da inganta ilimi,” inji shi.