Jam’iyyar APC za ta kawo dauki a Neja-Dalta – Faruk Adamu

Faruk Adamu, wani jigo a jam’iyyar APC da ya fito daga Jihar Jigawa, ya bayyana yadda jam’iyyarsa ke shirin kawo wa al’ummar Jihar Kuros Ribas dauki, a wajen taron yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Janar Muhammadu Buhari, a ziyarar da ya kai Kalaba, babban birnin Jihar Kuros riba. Ya ce, Alhamdulillahi, mun […]

Jam’iyyar APC za ta kawo dauki a Neja-Dalta – Faruk Adamu
Jam’iyyar APC za ta kawo dauki a Neja-Dalta – Faruk Adamu

Faruk Adamu, wani jigo a jam’iyyar APC da ya fito daga Jihar Jigawa, ya bayyana yadda jam’iyyarsa ke shirin kawo wa al’ummar Jihar Kuros Ribas dauki, a wajen taron yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Janar Muhammadu Buhari, a ziyarar da ya kai Kalaba, babban birnin Jihar Kuros riba.

Ya ce, Alhamdulillahi, mun gode wa Allah, mun gode wa mutanen Kuros riba, domin duk da gwamnatin jiha ta hana mu yin amfani da babban filin wasa Alhamdulillahi, mutane sun zo mun gode musu. Kuma kamar yadda muka fada canji ya zo Najeriya; canji ya zo Kuros riba, inda aka gaya mana yadda rigingimun siyasa da ake yi a wannan jiha. In Allah ya yarda za mu tabbatar da Muhammadu Buhari ya ci zabe a matsayin dan takararmu, kuma mutanen Kuros riba za su kawo canji.
Da aka tuntube game da yadda yake ganin karbuwar jam’iyyar a yankin Neja-Dalta, sai ya ce, kamar yadda maigidan mu yake fadi jiki magayi, kowa jikinsa ya gaya masa a kasar nan, idan kana so ka ci gaba da wahala ka zabi PDP; idan kana son tashin hankali ka zabi PDP. Idan kana son rashin wuta, rashin makaranta ka zabeta. Saboda haka wannan kadai ya isa ya nuna wa jama’a cewa canji ya zo, kuma kowa ya ji a jikinsa. In Allah ya kawo lokaci, kuma jam’iyyar APC ce za ta kafa gwamnati.
A cewarsa, yaya za a yi gwamnati ta bari mutanen ta ke fada da junansu. Dole mu sasanta Su, tunda yaren su daya, addinin su daya, babu wani gari da za a ce Gwamna Sanata Liyel Imoke a ce a mazabarsa, ana rikici, ana kashe mutane, amma ya kasa yin komai, ya kasa sulhunta mutane. Ina tabbatar wa mutane mu gwamnatin mu, ba za ta yi irin haka ba, kuma muna duba yadda aka gurbata tattalin arzikin yankin su, da kuma gurbata mahallinsu, inda ya lalata aikin gona; ya lalata noma da kiwon kifi. Za mu tabbatar kamfanonin da ke aikin hakar mai suna biyan su kudin jangali, da kuma biyan su hakkin su. Mun hana cin hanci da rashawa, mu tabbatar wa mutanen nan sun samu ruwan sha mai kyau da kifi mai kyau, don harkokin su na noma ya inganta.
Shi ma Sanata Hadi sarika, ya ce abin da muke son mu fada musu, cewa Jihar Kuros riba da can tana daya daga cikin jihohin da ke da man fetur da rijiyoyinsu wannan gwamnati ta dauke musu, ta bai wa wasu, amma babu inda ya kai nan talauci, bayan Allah ya albarkace su da abubuwan alheri. Babban abin da za mu yi, shi ne za mu kyautata musu, mu ga an daina kuntata musu, an kawar da cin hanci da rashawa; an gyara rayuwar al’umma. Sannan kudin da aka sace a dawo da su. Domin ayyukan raya kasa. Ba a sake mantawa da su ba. Mun dauke su ’yan kasa ne, kamar yadda kowane bangaren kasa yake, inji shi.
“A jihar ne Janar Muhammadu Buhari ya kori sojojin Kamaru, a lokacin da suka so mamaye wurin, inda ya yi nuni da cewa, mutane sun gamsu da jam’iyyar APC,” inji shi.