Jam’iyyar APGA ba ta Kiristoci ba ne kadai – Ibrahim Abu

Jam’iyyar APGA a Jihar Nasarawa ta musanta jita-jita da wasu ke yadawa a jihar cewa jam’iyyar ta Kiristoci ne kuma tana kyamar Musulmi. Mataimakin dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin jam’iyyar a zaben da ya gabata Malam Ibrahim Abu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Lafiya. Ya cewadanda […]

Jam’iyyar APGA ba ta Kiristoci ba ne kadai – Ibrahim Abu
Jam’iyyar APGA ba ta Kiristoci ba ne kadai – Ibrahim Abu

Jam’iyyar APGA a Jihar Nasarawa ta musanta jita-jita da wasu ke yadawa a jihar cewa jam’iyyar ta Kiristoci ne kuma tana kyamar Musulmi.
Mataimakin dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin jam’iyyar a zaben da ya gabata Malam Ibrahim Abu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Lafiya. Ya ce
wadanda ke yada jita-jitar cewa jam’iyyar tana kyamar Musulmi ba su yi wa jam’iyyar adalci ba inda ya ce jam’iyyar tana tafiya da kowa a jihar ba tare da la’akari da daga wane addini ya fito ba.
Malam Ibrahim Abu ya ce abokan adawar jam’iyyar daga Jam’iyyar APC ne ke yada jita-jitar da nufin bata mata suna, inda ya ce a yanzu haka shugaban Jam’iyyar APGA na jihar Alhaji Musa Sa’idu Bahaushe ne Musulmi, kuma Shugaban Matasa Abu Kamfani Musulmi ne sai kuma shi kansa Mataimakin dan takarar Gwamna Musulmi ne inda ya nuna mamaki kan yadda ake yada wannan jita-jita marar tushe.
Sai ya zargi Jam’iyyar APC da kasa cika alkawurran da ta yi wa al’ummar jihar cikin shekara biyar da ta yi tana mulkin jihar, inda ta koma tana yada jita-jita marar ma’ana.
Shugaban Jam’iyyar APGA a Jihar Alhaji Musa Sa’idu ya ce kodyake an kafa jam’iyyar a Kudu ne hakan ba yana nufin jam’iyyar ta Kiristoci ne kawai ba. Ya ba da mitsali cewa tsohuwar
Jam’iyyar NPP an kafa ta a Kudu ne amma ta samu karbuwa a tsohuwar Jihar Filato a nan Arewa. Sai ya bukaci al’ummar jihar su yi wasi da jita-jitar ake yadawa su ci gaba da ba APGA cikakken goyon baya domin a cewarsa jam’iyyar ce kadai za ta iya ceto su daga mummunan shugabanci da ake fuskanta a yanzu. Ya ce da zarar ta karbi ragamar mulki daga hannun APC bayan kotu ta kammala shari’ar zaben Gwamnan Jihar, al’ummar jihar za su ga bambanci.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista