Jam’iyyar GPN ta yi tir da zaben kananan hukumomin Kano

Jam’iyyar Green Party (GPN) ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin Jihar Kano a matsayin abin Allah wadai da kuma ci baya ga dimokuradiyya da aka dauki kusan shekara 20 ana gudanarwa a kasar nan.   A ranar Asabar da ta gabata ce Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KAINSEC) ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar, inda […]

Jam’iyyar GPN ta yi tir da zaben kananan hukumomin Kano

Jam’iyyar Green Party (GPN) ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin Jihar Kano a matsayin abin Allah wadai da kuma ci baya ga dimokuradiyya da aka dauki kusan shekara 20 ana gudanarwa a kasar nan.  

A ranar Asabar da ta gabata ce Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KAINSEC) ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar, inda Jam’iyyar APC ta lashe dukan kujerun kananan hukumomi 44 da na kansiloli 484.    

A cikin takardar da Jam’iyyar GPN ta fitar dauke da sa hannun Shugabanta, Alhaji Mannir Maisikeli, ta bayyana ranar 11 ga Fabrairu a matsayin rana mafi muni a tarihin siyasar jihar, lura da yadda hukumar zaben wacce ya dace ta gudanar da aiki bisa doka da oda amma sai ga akasin hakan.    

Jam’iyyar GPN ta ce ta yi mamaki game da yadda ta ji sanarwar sakamkon zaben inda Jam’iyyar APC ta ce wai ta lashe zaben ta hanyar samun kuri’a masu yawan gaske “wanann abin takaici ne, kuma karan-tsaye ne ga dimokuradiyya. Har ila yau abin kunya ne a fito a bayyana wannan sakamakon zaben da ya hadu da cikas ko wanda ya fi kama da wasan kwaikwayo,” inji GPN.

Jam’iyyar ta zargi APC da yin amfani da matasa wajen yin barazana ga jama’a tare da lalata akwatunan zabe ba tare da nuna damuwa ba. “Baya ga wananan kuma APC ta raba wa kananan yara da almajirai takardun zabe don su dangwala mata,” inji ta.

Ta ce ba za ta amince da sakamakon zabe ba.  

Sannan Jam’iyyar GPN ta yi kira ga Hukumar Zabe ta Jihar Kano ta yi gaggawar soke zaben tare da sake gudanar da sabon zabe idan ba haka ba za ta dauki matakin shari’a. 

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kano su adana duk wasu hujjoji da suke hannunsu wadanda ke nuni da yadda aka yi wa dimokuradiyya kisan gilla don amfanin wata rana, kasancewar ba za ta taba yarda da wannan sakamakon zaben kananan hukumomin ba.