Jam’iyyar LP na neman INEC ta soke zaben Ribas

Shugaban jam’iyyar Labour na kasa Julius Abure ya yi kira ga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke zaben da aka gudanar a Jihar Ribas, bisa zargin magudi da ya cewa jam’iyya mai mulki ta PDP ta tafka. Shugaban ya ce bayan kammala zabukan ranar Asabar ne, ‘yan daba suka far wa ma’aikatan zaben, suka […]

Jam’iyyar LP na neman INEC ta soke zaben Ribas

Shugaban jam’iyyar Labour na kasa Julius Abure ya yi kira ga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke zaben da aka gudanar a Jihar Ribas, bisa zargin magudi da ya cewa jam’iyya mai mulki ta PDP ta tafka.

Shugaban ya ce bayan kammala zabukan ranar Asabar ne, ‘yan daba suka far wa ma’aikatan zaben, suka kwace musu kayan aikin da suka hada da takardun rubuta sakamakoda na’urar BVAS.

Ya ce bayan kwace na’urar BVAS din, sun dura ma ta sakamakon jabu.

“Hakan ta faru a wurare irinsu Obio/Akpor, Khana, Eleme, Obigbo, Rumukoro da sauran rumfunan zabe a jihar da LP ke da yawan kuri’u.

“Gwamna Nyesom Wike ne ya fuskanci LP za ta yi nasara a rumfunan zaben yankinsa da kuri’a 323, shi ne ya sa a lalata zaben.

“BVAS din nan da haka ta faru da ita har tabbaci aka ba mu cewa babu yadda za a yi magudi da ita, sai ga shi mun ga akasin haka” in ji shi.

A don haka ya yi kira ga INEC ta bincika lamarin don hukunta masu laifi, sannan ta soke zaben a wuraren da abin ya shafa.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno