Jam’iyyar LP ta yi watsi da hukuncin kotu kan zaben Shugaban Kasa

Jam’iyyar ta bayyana takaicinta da hukuncin da alkalan suka yanke

Jam’iyyar LP ta yi watsi da hukuncin kotu kan zaben Shugaban Kasa

Peter Obi

Jam’iyyar LP ta bayyana takaicinta da korar kararta da kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban Kasa ta yi a ranar Laraba.

Kotun mai alkalai biyar da ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Tsammani dai ta yi watsi da kararrakin da LP da dan takararta, Peter Obi suka shigar.

Kotun dai ta ki amincewa da karar da LO ta shigar tana kakubalantar cancantar tsayawa takarar Bola Tinubu, da Mataimakinsa, Kashim Shettima, inda ta ce ba ta da tushe.

Sai dai da yake tsokaci a kan hukuncin, Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar na Kasa, Obiorah Ifoh, ya ce hukuncin da Kotun ta yanke ba ya kan doron doka, kuma ya saba da abin da mutane ke bukata.

Obiora ya ce, “’Yan Najeriya shaida ne a kan fashin da aka aikata ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, wanda a fadin duniya aka yi alla-wadai da shi, amma kotun ta ki karbar hakan.

“Ana kokarin yi wa tsarin Dimokuradiyya zagon kasa, kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai an dawo wa da mutane hakkinsu.

“Muna jinjina wa jajircewar lauyoyinmu da tawagarmu saboda rashin nuna tsoro wajen bayyana yadda tsarin shari’armu ya lalace. Za ku yi alla-wadai kawai da Dimokuraɗiyya ke ciki, amma har yanzu mun yarda da Najeriya a matsayin kasa,” in ji Obiora.

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara