Jam’iyyar Matan Arewa za ta dawo don bai wa mata Ilimi a Jigawa
Zamu da wo da jam’iyyar matan Arewa a Jahar Jigawa domin tsunduma mata cikin harkokin siyasa saboda mata su shiga a dama da su cikin tsarin mulkin kasar nan, saboda mata suna da tausayi da adalci fiye da maza a dangogin rayuwa ta yau da kullum. Jawabin hakan ya fito ne daga bakin Zainab Muhammad […]

Zamu da wo da jam’iyyar matan Arewa a Jahar Jigawa domin tsunduma mata cikin harkokin siyasa saboda mata su shiga a dama da su cikin tsarin mulkin kasar nan, saboda mata suna da tausayi da adalci fiye da maza a dangogin rayuwa ta yau da kullum.
Jawabin hakan ya fito ne daga bakin Zainab Muhammad S Fawa Kazaure, a wata hira da ta yi da wakilimmu a wannan makon, inda ta bayyana cewa, an samar da kungiyar ta matan Arewa ne tun lokacin Sardauna Ahmadu Bello, a lokacin yana fira-minista.
Kuma a wancan lokacin matansa ne suke rike da ita wannan kungiyar saboda fadakar da mata da taimakawa mata wajen hada kan matan Arewa baki daya. Ta ce yanzu haka lokaci ya yi da mata zasu dawo su sake hadewa wajen bayar da tasu gudunmawar dan ganin an sami cigaban kasa.
Hajiya Zainab ta kara da cewar ita wannan kungiya a halin yanzu ta sake dawo wa da karfinta, zata yi aiki a daukacin jihohin Arewacin kasar nan domin fadakar da mata kuma su sanya su shiga harkokin siyasa a dama da su a sha’anin mulkin kasar nan. “Dakta Famela Sadauki ita ce shugabar kungiyar ta kasa dake zaune a Kaduna kuma ita ce shugabar kungiyar a jahar Jigawa, mun bullo da kungiyar ne domin baiwa mata tarbiyya tare da cusawa masu akida su shiga cikin harkokin siyasa a dama da su.”
Ta kara da cewar idan lokaci ya yi za su fi mayar da hankali ne wajen sanya mata cikin harkokin neman ilimi, domin ita siyasa ba ta yiwuwa dole sai da ilimi ake cin moriyarta, kuma zasu tsaya sosai wajen kula da tarbiyyar yara kanana domin su ne manyan gobe.
Hajiya Zainab ta ci gaba da cewa, zasu tabbatar da cewa a zabe mai zuwa mata sun tsaya takarar mukamai daban-daban ciki har da kujerar gwamnoni da shugaban kasa da sauran matakan iko, saboda a cewarta mata sun fi maza adalci da iya tafiyar da tsarin shugabanci nagari, wannan ce tasa take da burin su ga sun saka mata a cikin tsarin tafiyar da shugabancin kasar nan.