Jam’iyyar NNPP ta dakatar da Kwankwaso daga cikinta

Jam’iyyar ta sanar da haka ne ranar Laraba

Jam’iyyar NNPP ta dakatar da Kwankwaso daga cikinta

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Kwamitin Amintattu na jam’iyyar NNPP na kasa ya dakatar dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar a zaben da ya gabata, Rabi’u Musa Kwankwaso, daga jam’iyyar.

Jam’iyyar ta kuma kori Kwamitin Zartarwa ma Kasa na jam’iyyar.

Kazalika, jam’iyyar ta sanar da nada Dokta Agbo Major a matsayin mai rikon mukamin Shugaban jam’iyyar na kasa, sai Ogini Olaposi a matsayin Sakataren riko da wasu mutum 18.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewar dakatarwar za ta yi aiki ne na tsawon wata shida.

An dai bukaci mambobin jam’iyyar ne su kada kuri’a yayin taron da aka yi a otel din Rockview da ke Apapa a Jihar Legas, kafin daukar matakin.

Idan za a iya tunawa, ko a ranar 24 ga watan Agusta, sai da jam’iyyar ta sanar da korar wanda ya kafa ta, Dokta Boniface Aniebonam.

Da yake yi wa ’yan jarida jawabi a karshen taron a Legas ranar Talata, Sakataren Kwamitin Aminitattun, Babayo Muhammad Abdullahi, ya zargi Kwankwaso da kulla alaka da Shugaban Kasa Bola Tinubu ba tare izininsu ba.

Kazalika, jam’iyyar ta ce tsohon dan takarar tata na alaka da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.

Jam’iyyar ta kuma ce ta tube wa Kwankwason rawaninsa na Jagoran jam’iyyar na kasa.

Sakataren Kwamitin ya ce dakatarwar na da alaƙa da yi wa Kundin Tsarin Mulkin jam’iyyar karon tsaye.