Jam’iyyar NPP mai mulki ta amince da shan kaye a Zaɓen Ghana

Tun gabanin bayyana sakamako a hukumance, jam’iyyar NPP mai mulki ta amince da shan kaye a Zaɓen Shugaban Ƙasar Ghana da aka gudanar a jiya Asabar. Ɗan takarar jam’iyyar, Mahamudu Bawumia ne ya amince da shan kaye a zaɓen cikin wani taƙaitaccen jawabi da ya yi wa manema labarai a yau Lahadi. Tinubu ya yi […]

Jam’iyyar NPP mai mulki ta amince da shan kaye a Zaɓen Ghana

Tun gabanin bayyana sakamako a hukumance, jam’iyyar NPP mai mulki ta amince da shan kaye a Zaɓen Shugaban Ƙasar Ghana da aka gudanar a jiya Asabar.

Ɗan takarar jam’iyyar, Mahamudu Bawumia ne ya amince da shan kaye a zaɓen cikin wani taƙaitaccen jawabi da ya yi wa manema labarai a yau Lahadi.

Bawumia wanda shi ne Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce bayan zaɓen da aka gudanar ranar Asabar a faɗin ƙasar hankulan jama’a sun karkata kan sanin samakon zaɓen.

“Saboda haka bisa ga bayanan da muka tattara a ɓangarenmu daga cibiyoyin tattara sakamako sun nuna cewa tsohon shugaban ƙasarmu, wanda ke takara a jam’iyyar NDC, John Dramani Mahama ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da gagarumin rinjaye,” in ji Bawumia.

Bawumia ya kuma ce jam’iyyar hamayya ta NDC ta kuma samu gagarumin rinjaye a majalisar dokokin ƙasar.

“Duk da cewa muna dakon sakamakon wasu mazaɓun majalisar dokokin ƙasar, amma ina da yaƙinin cewa babu abin da zai sauya wannan sakamako [rinjayen NDC a majalisa].

“Da wannan ne na kiran ɗan takarar jam’iyyar hamayya ta NDC, John Daramani Mahama domin na taya shi murnar kasancewarsa zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Ghana,” in ji shi.

Bawumiya ya bayyana cewa “al’ummar Ghana sun bayyana abin da ke zuciyarsu bisa sauyi da suke buƙata don haka na yi mubayi’a.”

Ɗan takarar jam’iyyar NDC mai adawa kuma tsohon shugaban kasar Ghana, John Mahama a shafinsa na X ya amsa tayar murnar da Bawumiya ya yi masa nan take.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra