Jam’iyyar Paul Biya ta yi karo da ’yan adawa

Jam’iyyar Shugaba Paul Biya ta yi karo da jam’iyyar adawa ta SDF a wajen yakin neman zabe. An samu rashin jituwa tsakanin RDPC na Shugaban kasa Paul Biya da kuma SDF ta Ni John Fru Ndi a birnin Bamenda, inda a kasarin magoya bayan jam’iyyar ta ‘yan adawa suke. A yayin da Gwamnati karkashin jagorancin […]

Jam’iyyar Paul Biya ta yi karo da ’yan adawa

Magoya bayan jam’iyyu na karawa da junaJam’iyyar Shugaba Paul Biya ta yi karo da jam’iyyar adawa ta SDF a wajen yakin neman zabe. An samu rashin jituwa tsakanin RDPC na Shugaban kasa Paul Biya da kuma SDF ta Ni John Fru Ndi a birnin Bamenda, inda a kasarin magoya bayan jam’iyyar ta ‘yan adawa suke.
A yayin da Gwamnati karkashin jagorancin Minista Paul Atanga Nji ta ce ta aika jami’an tsaro biranen Bamenda da kuma Santa, domin su tabbatar da zaman lafiya gabannin da kuma bayan zabe, saboda irin hatsaniyar da ake fama da ita a duk lokacin da aka gudanar da zabe.
Su kuma mabiya jam’iyyar SDF gani suka yi cewa babu ta yadda gwamnati za ta ce ta aika jami’an tsaro kusan 500, domin kula da gudanar da zabe. A ganinta, an yi amfani da su domin su jefa wa jam’iyya  mai mulki kuri’u, ganin cewa Minista Atanga Nji, wanda shi ne shugaban tawagar masu yi wa RDPC yakin neman zabe ya ce za su samu lashe wadannan zabubbuka da gaggarumin rinjaye. Abinda kuma bai yi wa SDF dadi ba.
Sakatariyar jam’iyyar SDF, Elisabeth Tamanjong da tarin wasu mabiya jam’iyyar suka fara yin tattaki na nuna rashin amincewarsu game da wannan yunkuri na Minista Atanga Nji.
Saboda yanayin da aka shiga, aka tsaida wani taro na gaggawa a ofishin Hukumar zabe na birnin Bamenda, inda mukaddashin Manajar Hukumar da mukaddashin Gwamna da kuma shugaban karamar Hukumar Bamenda ta farko suka halarta suka ba da haske game da abin da yake aukuwa.
Mukaddashin Manajar Hukumar zabe ya ce ya samu jerin sunanyen wasu jami’an tsaro kusan 360 wadanda ya ce sunan bukatar da aka kara sunansu a cikin kundin zaben, bayan sun yi rajista 66 ne kawai daga cikinsu suka samu katunansu alhalin kuma wasu 27 na rike da takardar shaidar rajista.