Jam’iyyar PDM na nan daram – Yahaya Kega

Shugaban Dattawa na Jam’iyyar PDM a Jihar Filato Alhaji Yahaya Kega ya ce jam’iyyarsu tana nan daram a dukkan mazabu da kananan hukumomi da jihohin Najeriya. Alhaji Yahaya Kega ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce suna nan suna shirye-shiryen tunkarar zabubbukan badi, kuma za su […]

Jam’iyyar PDM na nan daram – Yahaya Kega
Jam’iyyar PDM na nan daram – Yahaya Kega

Shugaban Dattawa na Jam’iyyar PDM a Jihar Filato Alhaji Yahaya Kega ya ce jam’iyyarsu tana nan daram a dukkan mazabu da kananan hukumomi da jihohin Najeriya.
Alhaji Yahaya Kega ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce suna nan suna shirye-shiryen tunkarar zabubbukan badi, kuma za su tsayar da ’yan takara a ko’ina a Najeriya a duk matakan da za a yi takara a kansu a badin.
Alhaji Kega ya ce yanzu a Najeriya jam’iyyyar ce ta uku, kuma ta samu karbuwa a ko’ina domin babu jihar da babu jam’iyyar.
Ya ce Jam’iyyar PDM tana da kyawawan kudurori na warware matsalolin da suke damun Najeriya a halin yanzu, kuma babu ruwanta da nuna bambancin addini ko kabila. Don haka ya yi kira ga al’ummar Najeriya su fito kwansu da kwarkatarsu su rungumi jam’iyyar don ta samu damar aiwatar da kudurorin da take dauke da su.
Da ya juya ga binciken zargin almundahanar kudin shiga da rarar man fetur na Jihar Filato har kimanin Naira biliyan 70 da Majalisar Dokokin Jihar take yi wa Gwamna Jonah Jang, Alhaji Kega ya ce majalisar taso ta makara kan binciken.
Ya ce ’yan majalisar su ne wakilin jama’ar jihar, don haka hakkinsu ne su binciki duk yadda aka kashe kudaden al’ummar jihar.
Ya ce bai kamata su zauna su yi shiru suna kallo sai yanzu da abu ya baci, duk da haka ya yi fata za su yi binciken tsakani da Allah don gano gaskiyar lamarin.