Jam’iyyar PDM za ta samar da ingantaccen shugabanci – Ibrahim Master
Ko’odinetan sabuwar Jam’iyyar PDM a Jihar Kebbi Alhaji Ibrahim Master Yalwa, ya ce jam’iyyar za ta samar ingantancen shugabanci a tsakanin wakilanta a jihar da kasa baki daya.Alhaji Ibrahim Master ya bayyana haka a lokacin da ya kira taron manema labarai a ofishinsa da ke Birnin Kebbi, ya ce “Jam’iyyar za ta dama da kowa […]
Ko’odinetan sabuwar Jam’iyyar PDM a Jihar Kebbi Alhaji Ibrahim Master Yalwa, ya ce jam’iyyar za ta samar ingantancen shugabanci a tsakanin wakilanta a jihar da kasa baki daya.
Alhaji Ibrahim Master ya bayyana haka a lokacin da ya kira taron manema labarai a ofishinsa da ke Birnin Kebbi, ya ce “Jam’iyyar za ta dama da kowa tare da nuna kyakkyawan shugabanci tun daga mazabu har zuwa na kasa.”
Ya ce, a matsayinsu na tsofaffin ’yan siyasa kuma aka damka musu nauyin shugabancin jam’iyyar za su tabbatar wa jama’an jihar cewa su’yan siyasa ne nagari.
Ya ce sabuwar jam’iyya za ta yi aikin da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar a tsakanin ’ya’yanta.
Alhaji Ibrahim Master ya ce za su kuma tabbatar da adalci ga jam’iyyun da suke son su hadu da su, “kofofin jam’iyyarmu a bude suke muna maraba da duk mai bukatar shiga jam’iyyar da masu ba da shawarwari masu ma’ana domin ci gaban kasa,” inji shi.