Jam’iyyar PDP ba ta da ikon zaba wa majalisa shugabanni – Lawal Rabi’u
dan Majalisar Tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u ya ce Jam’iyyar PDP ba ta da ikon zabar musu shugabanni.Alhaji Lawal Rabi’u ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu, inda duk da cewa abin da ya faru lokacin zaben shugabannin Majalisar Wakilai ya riga ya faru, […]
dan Majalisar Tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u ya ce Jam’iyyar PDP ba ta da ikon zabar musu shugabanni.
Alhaji Lawal Rabi’u ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu, inda duk da cewa abin da ya faru lokacin zaben shugabannin Majalisar Wakilai ya riga ya faru, “amma Jam’iyyar PDP ba ta da ikon ta ce sai ta zaba mana Shugaban Masu Rinjaye da Mataimakinsa da Mai Tsawatarwa da Mataimakinsa a wannan majalisa. Domin wannan hurumi ne na jam’iyyar da take da rinjaye a majalisa, don haka jam’iyyarmu ce take da hurumin zabar mana wadannan shugabanni. Kuma duk da na kwarai ba zai ki maganar uwarsa ba. Don haka mu muna bayan abin da uwar jam’iyyarmu ta APC ta ce mu yi a majalisar,” inji shi.
Ya ce tunda a zaben shugabancin majalisa, Allah Ya bai wa Yakubu Dogara kuma uwar jam’iyyarsu ta APC ta kawo sunayen mutum hudu da take so a ba su sauran mukaman majalisa, a nan suna tare da uwar jam’iyyar kuma duk abin da ta ce su yi shi za su yi.
Sai ya jawo hankalin ’yan uwansa ’yan majalisa da shi shugaban majalisa kan su kwantar da hankalinsu, su fahimci babu wanda ya je majalisar da sunansa kawai, “kowannenmu sai da ya sanya sunansa a karkashin wannan jam’iyya ta APC. Don haka ina ba da shawara mu bai wa jam’iyyarmu goyon baya da domin mu a samu ci gaba a wannan kasa. Domin na tabbatar uwar jam’iyyarmu ta APC ba za ta ba mu shawara kan abin da zai cutar da al’ummar kasar nan ba,” inji dan majalisar.
Alhaji Lawal Rabi’u, ya roki al’ummar kasar nan su ci gaba da addu’a Allah Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar a kasar nan. Mun yi imani idan aka samu zaman lafiya, za a samu ci gaba a gwamnatin Buhari.
Sai ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa akwai baraka a Jam’iyyar APC a karamar hukumarsa, inda ya ce kan ’ya’yan jam’iyyar a hade yake a yankin.