Jam’iyyar PDP ce ta kayar da kanta – Shugaban Matasa
Tsohon shugaban matasa na tsohuwar Jam’iyyar NPP reshen Jihar Filato kuma jigo a Jam’iyyar APC Alhaji Haruna Usman ya ce, Jam’iyyar PDP ce ta kayar da kanta a zabubbukan da suka gabata.Alhaji Haruna Usman ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce PDP ta kayar da kanta […]
Tsohon shugaban matasa na tsohuwar Jam’iyyar NPP reshen Jihar Filato kuma jigo a Jam’iyyar APC Alhaji Haruna Usman ya ce, Jam’iyyar PDP ce ta kayar da kanta a zabubbukan da suka
gabata.
Alhaji Haruna Usman ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce PDP ta kayar da kanta ne sakamakon rashin adalcin da shugabanninta suka yi wa magoya bayansu, inda suka ce tilas sai Goodluck Jonathn za a zaba don yi mata takara.
Ya ce a matakan jihohi kuma kowanne Gwamna ya tsaya ne cewa dole sai wanda yake so za a zaba don yi wa jam’iyyar takara, don haka ne jama’ar Najeriya suka yi masu tawaye.
Alhaji Haruna Usman ya ce babban abin da ya sa Jam’iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zaben, shi ne ta ba kowa ’yancinsa a cikin jam’iyyar, lokacin da ta gudanar da zaben fidda-gwani ta hanyar ba kowane dan takara ’yancinsa tare da barin jama’a su zabi wanda suke so.
Tsohon Shugaban Matasan ya ce tun daga kan yadda aka zabi Janar Buhari a zaben fidda-gwani da aka gudanar a Legas, APC ta nuna cewa dole ne a yi gaskiya a Najeriya. Ya ce wannan mataki da jam’iyyar ta dauka ne ya kawo mata gagarumar nasara a Najeriya.
Ya yi kira ga wadanda suka fadi a zabubbukan da aka gudanar, su rungumi kaddara kamar yadda Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi.