Jam`iyyar PDP karamar magana ta zama babba

Ya zuwa yanzu masu ruwa da tsakiya na kasa baki daya na babbar jam`iyyar PDP mai mulki da gwamnatin tsakiya da kuma gagarumin rinjaye a cikin yawan gwamnonin jihohi da `yan majalisun dokoki na kasa suna can suna  ci gaba da yin tarurrukan neman sulhu, tun bayan da rikicin da jam`iyyar ta dade tana fama […]

Jam`iyyar PDP karamar magana ta zama babba
Jam`iyyar PDP karamar magana ta zama babba

Ya zuwa yanzu masu ruwa da tsakiya na kasa baki daya na babbar jam`iyyar PDP mai mulki da gwamnatin tsakiya da kuma gagarumin rinjaye a cikin yawan gwamnonin jihohi da `yan majalisun dokoki na kasa suna can suna  ci gaba da yin tarurrukan neman sulhu, tun bayan da rikicin da jam`iyyar ta dade tana fama da shi ya bayyana karara a wajen babban taron jam`iyyar na musamman  na kasa baki daya da jam`iyyar ta gudanar a ranar Asabat 31 ga watan Agustan da ya gabata a Abuja.
 A waccan rana ce rikicin da jam`iyyar ta PDP ta dade tana fama da shi tsakaninta da gwamnoninta ya fito karara a idanun duniya, a lokacin da wasu gwamnonin jam`iyyar  su bakwai a karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, suka fice daga dakin babban taron jam`iyyar, ba kuma inda suka tsaya sai cibiyar taro ta Shehu Musa Yar`adu dake Abujar, inda suma suka gudanar da babban taronsu na kasa, suka kuma zabi sababbin shugabanninsu na zartasawa a karkashin jagorancin Alhaji Abubakar Kawu Baraje, wanda yake tsohon shugaban riko na kasa baki daya na jam`iyyar PDP, kafin waccan rana, suka kuma bayar da shelar kafa sabuwar jam`iyyar PDP.
Tun  kafin ranar babban taron PDP, wasu  gwamnoni shidda  na jam`iyyar, wadanda suka hada da Alhaji Sule Lamido na jihar Jigawa da Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako na Jihar Sakkwato da Cif Rotimi Ameachi na jihar Ribas (shugban kungiyar gwamnonin kasar nan) da Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso na Jihar Kano da Alhaji Murtala Nyako na Jihar Adamawa da Dokta Ma`azu Babangida Aliyu na Jihar Neja, (shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa), wadanda suka dade suna rigima da uwar jam`iyyar ta kasa, akan zargin shugabancin Bamanga Tukur da kama karya, bisa daurin gindi shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan.  A ranar babban taron ne  Gwamnan Jihar Kwara  Alhaji Ahmed Abdullfatah, ya zama cikon na bakwai a tafiyar gwamnonin.
A yanzu maganar da ake akwai `yan Majalisar Dattawa 22, da na Majalisar Wakilai 57, da suka bar jam`iyyrar PDP suka rungumi sabuwar PDP.ana kuma kyautata zaton wasu ma na nan tafe idan har jayayyar ta dore. A irin wannan hali aka ji Gwamnan Jihar Kano,  Dokta Rabi`u Kwankwaso a wata hira da ya yi da sashen Hausa na gidan Radiyon BBC, a ranar Juma`ar makon da ya gabata, yana fadin cewa har yanzu ba su da aniyar barin jam`iyyarsu ta PDP, amma sai ya kara da cewa muddin jam`iyyar ba ta biya masu bukatunsu ba, to kuwa ba su da wani zabin da ya wuce su shiga jam`iyyar adawa ta APC, yana mai karawa da cewa akasarin shugabannin jam`iyyar ta APC ai abokanmu ne. Wannan ikirari yana nuna tura ta kai bango.
Gwamnan na Kano ya kuma fadi a waccan hira cewa bayan su gwamnoni bakwai da suka balle akwai gwamnoni da `yan Majalisun Dokoki na kasa da dama da suke goyon bayansu akan rashin dacewar shugabancin na Alhaji Bamanga Tukur. Da wannan bayani na Gwamna Kwankwaso mai karatu za ka iya fahimtar cewa gwamnonin nan suna da wata manufa ta boye, kuma kamar yadda Shugaba Dokta Goodluck Jonathan da wasu makarrabansa suka sha fadi, wannan tinja-tinja da ake fama da ita a jam`iyyar ta PDP, duk ana yinta ne don zabubbukan shekarar 2015, in Allah Ya kai mu.
 Dukkan yunkurin da akai a baya kamar na ganawar da shugaban kasa ya yi da wadancan gwamnoni da wanda Alhaji Bamanga ya yi da su da kewayen da suka yi na saduwa da wasu daga cikin tsofaffin shugabannin kasa dana jam`iyyarsu don neman maslaha ka iya cewa ta faskara wajen samun daidaituwa. Yanzu abin da ya rage  ake kuma tsammanin shi zai kawo karshen rikicin shi ne yunkurin da wadda tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ke ta karkashin Kwamitinsa da ya kunshi wasu daga cikin dattawan jam`iyyar ta PDP irinsu tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida da shugaban Kwamitin amintattu na jam`iyyar Cif Tony Anenih da tsofaffin jam`iyyar na kasa guda biyu, wato Sanata Banarbas Gemade da Sanata Ahmadu Ali, ganawar da aka yi a ranar juma`ar da ta gabata da bangarorin jam`iyyun biyu, amma aka tashi ba a cimma wata maslaha ba.
 A waccan ganawa ce aka ce bangaren sabuwar PDP din ya mikawa tsohon shugabn kasa Cif Obasanjo sanarwar bayan taron da gwamnonin PDP 20, suka yi da shugaba Jonathan a cikin watan Disamban shekarar 2010, sanarwar bayan taron da ta amince shugaba Jonathan ya yi takarar 2011, wato ya karasa zangonsa na biyu a shekarar 2014, bisa ga tafiyar mulkinsu na shi da marigayi Alhaji Umaru Musa Yar`aduwa. Sanarwar bayan taron da Gwamnan Jihar Neja ya fara ambatata a watannin baya, amma kuma tun wancan lokacin shugaba Jonathan dana kusa da shi kai har ma da al`ummarsa na yankin Neja Delta suke ta karya samuwarta.
Mutum bai tara sa ni da Allah ba, amma da sai in ce gaba gadi shiri ba zai yiwu ba tsakanin Jam`iyyar PDP da sabuwar PDP, ba don kome ba kuwa, sai don bisa ga la`akari da cewa shi tsohon shugaban kasa Obasanjo bai shiga wannan rigima da wasu suke zargin shi ya kitsata, sai don ya sake samun dama ya kawo nasa gwanin a cikin shugabancin kasar nan a shekarar 2015, a inuwar jam`iyyar PDP, tunda yanzu kowa ya san sun karya kara da shugaba Jonathan, suna kuma zaman doya da manja.
 Wani hanzarin kuma shi ne akasarin gwamnonin da suka kafa sabuwar PDP `yan gidan Cif Obasanjo ne, daya daga cikinsu wai suke kwadayin a yi wa mataimakin shugaban kasa a shekarar 2015. A gefe dada kuma kowa ya sa ni cewa ba a ga maciji tsakanin Cif Obasanjo da tsohon mataimakinsa Alhaji Atiku Abubakar, haka labarin yake tsakaninsa da tsohon shugaban kasa Janar Babangida, bare kuma tsofaffin jam`iyyar PDP Sanata Ahmadu Ali da Sanata Barnabas, amma yanzu ga su suna shan inuwa daya har wai suna batun yadda za a ceto kasar nan. Mai karatu kasan akwai magana. Sai dai mu ce Allah Ya taimaki mai gaskiya, Ya ba mu shugabanni na gari amin.