Jam’iyyar PDP ta dakatar da Bafarawa saboda zargin yi mata zagon-kasa

Wasu shugabannin Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato sun ba da sanarwar dakatar da tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa daga jam’iyyar bisa zarginsa da yi wa jam’iyyar zagon-kasa da kuma yi mata rashin biyayya,Wata sanarwa da bangaren jam’iyyar na PDP ya bayar ta hannun Mataimakin Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PDP reshen Jihar, Alhaji […]

Jam’iyyar PDP ta dakatar da Bafarawa saboda zargin yi mata zagon-kasa
Jam’iyyar PDP ta dakatar da Bafarawa saboda zargin yi mata zagon-kasa

Wasu shugabannin Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato sun ba da sanarwar dakatar da tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa daga jam’iyyar bisa zarginsa da yi wa jam’iyyar zagon-kasa da kuma yi mata rashin biyayya,
Wata sanarwa da bangaren jam’iyyar na PDP ya bayar ta hannun Mataimakin Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PDP reshen Jihar, Alhaji Shehu dan Ya’u Sirajalo ya rarraba wa manema labarai ta zargi tsohon Gwamnan da kakkane komai na jam’iyyar da maida ita tamkar kayansa na gado.
Sanarwar ta nemi shugaban jam’iyyar ta jihar, Alhaji Ibrahim Milgoma da ya yi nesa da tsohon Gwamnan kan wannan matakin da suka dauka domin maido da martabar jam’iyyar a jihar.
Takardar wadda wadansu manyan shugabanin jam’iyya suka sanya wa hannu da suka hada da Hajiya Kulu Rabah Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP ta Jihar da wasu mutum goma ta bukaci a kira taron gaggawa na jam’iyyar don fito da hanyar da za a yi gyara tare da maido da darajar jam’iyyar a jihar.
 Sai dai a martanin da shugaban jam’iyyar na jihar Alhaji Ibrahim Milgoma ya mayar kan sanarwar ya nemi a yi watsi da wannan bayani da ya bayyana na masu yunkurin janyo rikici da haddasa rudu a cikin jam’iyyar domin biyan bukatar kansu.
Shugaban Jam’iyyar ya zargi wasu daga cikin masu sanya hannu a cikin takardar da cewa sun dade da canja sheka zuwa Jam’iyyar APC kuma suna tare da gwamnatin APC a Jihar Sakkwato.