Jam’iyyar PDP ta Jihar Kebbi ta gargadi Ma’ajin Jam’iyyar na kasa
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kebbi, ta ja kunnen Ma’ajin Jam’iyyar na kasa Alhaji Buhari Bala bisa abin da ta kira katsalandar da yake yi game da shugabancin jam’iyyar a jihar.Bayanin haka ya fito ne daga bakin Jami’in Hulda da Jama’a na Jam’iyyar reshen jihar Alhaji Ibrahim Umar Ummai a wani taron manema labarai da jam’iyya […]
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kebbi, ta ja kunnen Ma’ajin Jam’iyyar na kasa Alhaji Buhari Bala bisa abin da ta kira katsalandar da yake yi game da shugabancin jam’iyyar a jihar.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Jami’in Hulda da Jama’a na Jam’iyyar reshen jihar Alhaji Ibrahim Umar Ummai a wani taron manema labarai da jam’iyya ta kira a Birnin Kebbi.
Alhaji Ibrahim Umar Ummai ya ce uwar Jam’iyyar PDP ta kasa da ke Abuja ne ta ba su dama su yi zaben cike-gurbi na shugabancin jam’iyyar saboda shugaban da ta nada ya bar jam’iyyar, sun kuma zabi wanda jama’a ke so ya kuma dace ya shugabanci jam’iyyar.
Alhaji Ibrahim Ummai ya ce, bayan ’ya’yan Jam’iyyar PDP sun zabi wanda suke so ya shugabanci jam’iyyar wato Alhaji Musa Ibrahim dan-Illela, sai bayan mako biyu suka ji wadansu na yawo da takardu cewa uwar jam’iyya ta kasa ta rubuto wai ta zabi wani Alhaji Ali Bagudo a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar.
Ya ce da suka binciki inda takardar ta fito sai suka samu labarin cewa Alhaji Buhari Bala Ma’ajin Jam’iyyar PDP ta kasa kuma dan asalin Jihar Kebbi na da hannu a rubuto takardar cewa Alhaji Ali Bagudo ne shugaban jam’iyyar a jihar.
Ya yi kira ga Alhaji Buhari Bala ya bar kawo musu rudani a cikin jam’iyyar a jihar, ya tsaya can su ’yan Abuja ne, kuma ya ce ko gobe za a sake zabe in Allah Ya yarda Alhaji Musa Ibrahim dan-Illela ne zai sake cinye zaben.
Alhaji Ibrahim Ummai, ya jawo hankalin shugabannin Jam’iyyar PDP na kasa su tuna irin wannan katsalanda da wadansu shugabannin PDP ke yi, na nada wanda jama’a ba su so ya kara kawo faduwarta a zabe, “Don haka muke kara kira ga shugabanin PDP na kasa su shawo kan matsalar da ke son faruwa a cikin Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi kafin abin ya yi muni,” inji shi.