Jam’iyyar PDP ta karkasa inda shugabanninta za su fito

Jam’iyyar PDP ta karkasa yadda za a zabi shugabanninta daga shiyyoyin kasar nan a babban taronta na kasa da za ta gudanar a ranar 21 ga watan Mayu mai zuwa.Kwamitin tsara rabon mukaman a karkashin Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom wanda ya gana a Uyo fadar Jihar Akwa Ibom a ranar Asabar ya mika […]

Jam’iyyar PDP ta karkasa inda shugabanninta za su fito
Jam’iyyar PDP ta karkasa inda shugabanninta za su fito

Jam’iyyar PDP ta karkasa yadda za a zabi shugabanninta daga shiyyoyin kasar nan a babban taronta na kasa da za ta gudanar a ranar 21 ga watan Mayu mai zuwa.
Kwamitin tsara rabon mukaman a karkashin Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom wanda ya gana a Uyo fadar Jihar Akwa Ibom a ranar Asabar ya mika kujerar Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa ga shiyyar Arewa maso Gabas, yayin da Na’ibin Shugaban Jam’iyyar na kasa zai zakuda zuwa Kudu maso Kudu, sai kuma Sakataren Jam’iyyar zai zauna a Kudu maso Yamma.
Mukamin Sakataren Watsa Labari da aka tura wa Kudu maso Gabas a shekarar 2012, yanzu an mika shi ga Kudu maso Yamma, yayin da Shugabar Mata aka ba Arewa maso Yamma maimakon Kudu maso Gabas.    
Sai kuma Ma’ajin Jam’iyyar da ke yankin Arewa maso Yamma tun shekarar 2012 yanzu ya koma Arewa ta Tsakiya, yayin da ake sa ran Kudu maso Gabas ta fitar da Sakataren Tsare-Tsare wanda a yanzu ke hannun Arewa maso Yamma.
Sai dai wannan shawara tana bukatar amincewar bangarorin jam’iyyar kafin ta fara aiki.
Idan jam’iyyar ta amince da wannan tsari, Kakakin Jam’iyyar PDP ta kasa, Olisa Metuh da Shugabar Mata Misis Kema Chikwe, sai dai su nemi wasu mukaman ko kuma su gaza komawa cikin kwamitin gudanarwar jam’iyyar.
Sauran wadanda lamarin ya shafa sun hada da Ma’ajin Jam’iyyar Alhaji Buhari Bala da Sakataren Tsare-Tsare Alhaji Abubakar Mustapha.