Jam’iyyar PDP ta ki amincewa da rantsar da dan takarar APC Shugaban Karamar Hukuma a Kaduna
A ranar Talata ce ’ya’yan Jam’iyyar PDP da suka hada da shugabanninta da sauran masu ruwa-da-tsaki daga Karamar Hukumar Jaba da ke Kudancin Jihar Kaduna suka nuna rashin amincewarsu da rantsar da dan takarar shugaban Karamar Hukumar Jaba a karkashin Jam’iyyar APC, Benjamin Jock bayan tsawon lokaci ana tafka shari’a. Godfery Ali Gaiya, tsohon dan Majalisar […]
A ranar Talata ce ’ya’yan Jam’iyyar PDP da suka hada da shugabanninta da sauran masu ruwa-da-tsaki daga Karamar Hukumar Jaba da ke Kudancin Jihar Kaduna suka nuna rashin amincewarsu da rantsar da dan takarar shugaban Karamar Hukumar Jaba a karkashin Jam’iyyar APC, Benjamin Jock bayan tsawon lokaci ana tafka shari’a.
Godfery Ali Gaiya, tsohon dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Jaba da Zangon Kataf wanda ya jagoranci sauran ’ya’yan PDP, ya ce an tafka kura-kurai kuma an yi gaggawar rantsar da dan takarar APC maimakon Phillip Gwada na PDP wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranar 6 ga watan Maris din bara.
Mista Gaiya tare da Bisalla sun bayyana takaicinsu yayin ganawarsu da manema labarai kan rantsar da dan takarar APC da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta yi alhali shari’arsu na nan gaban kotun sauraron shari’ar zabubbuka.
Sun kara da bayyana cewa bai kamata hukumar zabe ta zama ta dauki bangare ba suna masu cewa kuri’un da dan takarar APC, Jock ya samu duka-duka dubu 7, 054 yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Gwada ya samu kuri’a dubu 17, 967.
“Mun fara shiga cikin halin rashin tabbas ne yayin da muka iso ofishin Hukumar SIECOM ta Jihar Kaduna a ranar 7 ga Yunin bara tare da jami’an Hukumar SIECOM daga Karamar Hukumar Jaba, amma sai aka shaida mana cewa wani Mista Ben Kure, (Sarakatan Kamfen na Malam Nasir El-Rufa’i) ya zo wa hukumar sakamakon zaben.” Suna masa tambayar ta yaya za a yi a zo da kayayyakin zabe a rana guda a tantance a kada kuri’a a kidaya na gundumomi guda goma kuma a sanya hannu sannan a kwashe su duka a dauka daga Jaba har Kaduna cikin rana guda.”
A karshe sun yi kira ga hukumar ta bai wa mutanen Jaba hakkinsu da suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka sha rana da iska suka zaba wa kansu wanda suke so ya shugabance su.
Sannan sun yi kira ga jama’ar Karamar Hukumar su kwantar da hankalinsu su guji duk wani abu da ka iya tayar da hatsaniya kamar yadda aka san su da son zaman lafiya.