Jam’iyyar PDP ta rungumi kaddara kawai a Taraba – Napoleon Adamu
Sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP a Jihar Taraba, Mista Napoleon Adamu, wanda jam’iyyar ta kora saboda nuna gamsuwa da hukuncin kotun sauraran karar zaben gwamna da ta sauke gwamnan Jihar Taraba, ya ce jam’iyyar PDP ita ce ta jawo wa kanta matsalar da ta samu kanta a ciki. Ya ce kamata ya yi jam’iyyar […]
Sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP a Jihar Taraba, Mista Napoleon Adamu, wanda jam’iyyar ta kora saboda nuna gamsuwa da hukuncin kotun sauraran karar zaben gwamna da ta sauke gwamnan Jihar Taraba, ya ce jam’iyyar PDP ita ce ta jawo wa kanta matsalar da ta samu kanta a ciki.
Ya ce kamata ya yi jam’iyyar PDP a Taraba ta yi waiwaye adon tafiya don gyara kura-kuran da ta tafka a baya, wanda ya jefa ta a cikin halin da ta samu kanta a ciki yanzu, ta daina bata lokacin ta zuwa kotunan daukaka kara, domin alkalami ya bushe.
Ya shaida wa wakilin Aminiya a wata hira, cewa, tun lokacin da jam’iyyar ta ki gudanar da zaben fidda dan takarar gwamna a Jalingo fadar Jihar Taraba, kamar yadda dokar zabe ta tanada ya fadakar da cewa, za a samu matsala a gaba, kuma ga shi an samu matsalar a yanzu.
Ya kara da cewa, ya bayar da shawarar cewa, ‘ka da akai zaben fidda dan takarar gwamna zuwa Abuja,’ domin yin haka ya saba wa dokar zabe, amma jam’iyyar ta ki bin wannan shawara tashi.
Mista Napoleon Adamu, ya ce to ga shi kotu ta kori gwamnan kan kin gudanar da zaben fidda dan takarar gwamna, kamar yadda dokar zabe ta tanadar.
Ya kara da cewa akwai lokacin da ya bayar da sanarwar cewa, dukkan wakilan da za su gudanar da zaben fidda dan takaran gwamna su hallara a fadar Gwamnantin Jihar Taraba, wato Jalingo, don gudanar da zaben fidda da ’yan takara, sai Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar Mista bictor Bala Kona ya bai wa kwamishinan ’yan sandan jihar na wancan lokaci umurnin ya gayyace shi.
Korraran sakataren watsa labaran na PDP ya ce, kwamishinan ’yan sandan ya tsare shi har na tsawon sama da awoyi shida ana yi masa tambayoyi kan cewa, wa ya ba shi umurnin ya bayar sanarwar za a gudanar da zaben fidda dan takarar gwamna a Jalingo.
A cewarsa, shugaban jam’iyyar na gudanar da jam’iyyar ta PDP a Jihar Taraba tamfar mallakar sa, sai abin da yake so ne kawai za a yi ba mai ikon cewa ufan.
Ya ce kalaman da ya furta cewa, ba a gudanar da zaben fidda da dan takarar gwamna a Jalingo ba ai gaskiya ne, kuma ba shi kadai ya furta haka ba.
A cewar sa, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Adamu Mu’azu da Hukumar Zabe ta kasa duk sun fadi cewa ba a gudanar da zaben a Jalingo ba.
Ya ce ya yi mamakin ganin yadda ’yan jam’iyyar ta PDP a jihar suka dauki maganarsa da zafi duk da kasancewar gaskiya ce ya fadi.
Mista Napoleon Adamu ya kara da cewa abin da ya kamata jim’iyyar ta PDP ta yi shine ta rungumi kaddara, ta bar magana daukaka kara kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke.
Ya bayyana cewa korar da akayi masa daga mukaminsa hauka ne da rashin bin tsarin dokokin jam’iyyar ta tanada kan hanyar da za a bi wajen ladabtar da jam’iyya in yayi laifi.
Mista Napoleon Adamu Ya kara dacewa yan jamiyyar basu bashi dama kare kansa ba sai kawai ya ji a kafafan watsa labarai cewa an koreshi daga jamiyyar.
Y ace irin wannan salon shugabanci na kama karya na shugaban jam’iyyar a jihar ya sa magoya bayan jam’iyyar ke ta barin jam’iyyar a jihar suna komawa wata jamiyya.
Da yake Magana kan kalamon da Mista Napoleon Adamu ya yi shugaban jam’iyyar na Jihar Taraba Mista bictor Bala Kona ya ce nuna amincewa da hukuncin da kotun ta zattar da shi wanda tsohon sakataren watsa labarai na jamiyyar na jihar yayi ya nuna cewa dama shi ya dade yana yi wa jam’iyyar ta PDP zagon kasa.
“Duk ’yan jam’iyyar PDP sun ki amincewa da hukuncin kotun sai Napoleon Adamu ne kawai ya fita a kafafan watsa labarai ya bayyana gamsuwarsa da wannan hukunci, hakan ya nuna a fili da ma shi ba dan jam’iyyar PDP na gaskiya ba ne,” inji shi.
A cewar Mista bictor Bala Kona, Koran Mista Napoleon ya zama tilas, domin kalamansa abin kunya ne ga duk dan jam’iyyar PDP ba a Jihar Taraba kadai ba, har ma da kasa baki daya.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa, zuwa yanzu kananan hukumomin Takum da Ussa ke kan gaba wajen daukan matakin ladabtar da duk wani ma’aikaci da aka gano ‘ya yi bikin murnar hukuncin kotun.’
Ana zargin cewa gwamnatin jihar ce ta bayar da umurnin a zakulo duk wani ma’aikacin da ya gudanar da biki na murnar yanke hukunci da kotun ta yi, kuma an ce tuni aka dakatar da albashin irin wadannan ma’aikata.