Jam’iyyar PDP ta saba da rikita-rikitar cikin gida – Abdulmalik Mahmood

Alhaji Abdulmalik Mahmood Baraden Katagum, tsohon shugaban karamar hukuma ne har karo uku kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi a lokacin mulkin Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu daga 1999 zuwa 2007, daya ne daga cikin wadanda aka kafa Jam’iyyar PDP da su a jihar da kasa baki daya a tattaunawarsa da wakilinmu a Bauchi, ya yi […]

Jam’iyyar PDP ta saba da rikita-rikitar cikin gida – Abdulmalik Mahmood
Jam’iyyar PDP ta saba da rikita-rikitar cikin gida – Abdulmalik Mahmood

Alhaji Abdulmalik Mahmood Baraden Katagum, tsohon shugaban karamar hukuma ne har karo uku kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi a lokacin mulkin Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu daga 1999 zuwa 2007, daya ne daga cikin wadanda aka kafa Jam’iyyar PDP da su a jihar da kasa baki daya a tattaunawarsa da wakilinmu a Bauchi, ya yi fashin baki game da rikita-rikitar da ta addabi PDP a matakin kasa da kuma matsalar hare-haren tsagerun Neja-Delta:

Me za ka ce game da rikita-rikitar da ta addabi jam’iyyarku ta PDP?
Abin da zan fada shi ne jam’iyyarmu ta PDP tun lokacin da aka kafa ta ta saba da rikita-rikitar cikin gida da sauran masu tada kayar-baya a bayan fage. Mun shekara 16 muna mulki a Najeriya kowa ya ga kamun ludayinmu mun yi kura-kurai a wasu wuraren. Kuma ina so ’yan Najeriya su fahimci cewa PDP ta saba da shiga garari sabanin wasu jam’iyyu, amma tabbas kafin zaben shekara ta 2019 za mu gyara dukkan kura-kuran da muka aikata a baya. Duk dan Jam’iyyar PDP ko ya fita daga cikinta ya koma wata jam’iyya zuciyarsa na PDP domin manufofinmu suna da kyau sannan muna da ’yan siyasa masu kyautata wa mutanen da suka zabe su. Akwai wadanda suke zaune a cikin jam’iyya ba su da wani aiki sai haddasa fitina a bayan fage domin ta haka suke cin abinci, akwai kuma masu neman kudi ruwa a jallo. Ba zan fadi lokacin da za mu fita daga cikin wannan rikita-rikita ba, amma dai na san yanzu ne talakawan Najeriya suka fahimci amfanin ’yan PDP. Duk dan PDP na gaskiya ko ya fita daga cikinta idan aka buga gangar siyasa sai ya dawo gidansu, PDP tana da wani sinadari ne daga Allah ko mutum ya dawo ba a yi masa bi-ta-da-kulli. Zaben shekara ta 2015 mutane sun mai da zaben kamar tashin kiyama amma yanzu ’yar manuniya ta nuna, ko gobe aka shirya zabe ina tabbatar maka cewa PDP ne za ta sake kafa gwamnati tun daga matakin kasa har zuwa jihohin kasar nan. Mutane sun yi fushi da PDP a shekarun baya amma yanzu kuma za mu ci gaba da ba da hakuri ga ’yan Najeriya a zabi PDP a shekara ta 2019.
Me ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ga ’yan Arewa?
Ba zan ce ya yi wa ’yan Arewa kadai ba, kasar baki daya ya kamata a dauka ta haka za mu samu ci gaba da hadin kai. Jam’iyyarmu ba daya ba ce da Buhari yana APC ni kuma ina PDP, tattakin azikin kasar nan ba zai taba bunkasa ba har sai an samu wutar lantarki na sa’o’i 18 zuwa sama a kowace rana. Bayan haka sai batun bunkasa aikin noma da kiwo shi ma ba zai yi nasara ba, idan ana fama da karancin wutar lantarki, tattalin arzikin duniya yana tangal-tangal haka masana ke fada.
Me za ka ce game da talauci da ya addabi ’yan Najeriya?
Dole talauci ya addabi ’yan Najeriya a halin yanzu domin an dogara ne da man fetur har matar da take kauyenmu na Abdallawa ta dogara ne da man fetur da zarar an kara Naira 10 a kudin mai komai sai ya yi tsada a kasar nan. Idan man fetur ya yi tsada ’yan dako ma za su kara kudi, masu motoci za su kara kudi ga fasinjoji, kayan abinci ma dole ya yi tashin gwauron zabo tunda har yanzu mun dogara ne da shigo da mai daga kasashen waje dole mu fuskanci dimbin matsaloli. Yanzu haka ana saida Dala sama da Naira 360 a kasuwannin bayan fage kuma da Dala ake cinikin man fetur a kasuwannin duniya ya kamata a bunkasa aikin noma a rage dogaro da mai.
Mene ne fahimtarka kan sababbin hare-haren da tsagerun Neja-Delta (Abengers) ke kai wa bututun mai?
Kafin in ba da amsar wannan tambaya ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa a matsayina na tsohon Mataimakin Gwamna na yi aiki a yankin Neja-Delta na sama da shekara uku na san wasu abubuwa da ’yan Arewa da dama ba su sani ba. Akwai dimbin kungiyoyin tsageru a yankin Neja-Delta amma wasu sun fi sanin Abengers domin su ne suka fito kwanan nan kuma suna ci gaba da kai munanan hare-hare kan bututun mai. Gwamnatin Tarayya tana ba yankin Neje-Delta kashi-13 daga cikin kudin da ake samu daga man fetur. Bayan haka an kafa musu Ma’aikatar Raya Yankin Neja-Delta tag a Hukumar Raya Yankin Neja-Delta (NDDC), kamfanonin da suke aiki a yankin suna ba su wani kaso daga cikin kudIn da suke samu. Akwai wadansu ayyuka sama da 1,500) wanda NDDC ke aiwatarwa a yankin, ba na shakka ka buga wannan a jarida. karya ne mutanen Neja-Delta su ce ana cutarsu, duk abubuwan da ya kamata a yi musu ana yi musu, amma ba sa gani. Ya kamata kungiyar Abengers su je su tambayi kudin da Jihar Akwa-Ibom take samu duk karshen wata da kuma kudin da Jihar Bayelsa take samu.
Wasu hanyoyi ya kamata a bi domin magance wannan matsala ta yankin Neja-Delta?
Ya kamata ’yan siyasar yankin su rika fada musu gaskiya domin suna daga cikin wadanda suke rudarsu, saboda haka suke ci gaba da tayar da kayar baya, yanzu ba na cikin gwamnati akwai wasu jawabai da ba ni da su saboda harka ce da ta shafi tsaro. Duk wanda ya yi aiki a yankin ya san matsalolin da suke fuskanta mutane ne masu son tara kudi. Akwai wani lokaci da za mu shiga wani yanki duk kauyen da muka zo, sai mun ba da kudi na matasa da tsofaffi da sarakunan yankin kafin su bar mu, mu wuce duk dan kwangila da ke yankin ya san abin da nake fada gaskiya ne. Shekara uku ina aiki a NDDC a yankin Neja-Delta na san abin da ke faruwa ciki da waje, ba wanda zai ba ni labari ba na mamakin manyan makaman da suke amfani da su, an jima ana shigo da makamai, kasar nan abar tausayi ce. Akwai wadanda suke cewa ya kamata Shugaba Buhari ya fara tono man fetur a Arewa, aikin tonon mai ba kamar tonon rijiya ba ne, domin abu ne mai matukar wahala bayan an tona dole a nemi hanyar da za a fita da shi zuwa wata kasa. Gwamnatin Najeriya da Kamfanin NNPC ba su da kudin da za su tono man fetur a Arewa a halin yanzu, ’yan kasuwa ba su da kudin da za su jari domin a tono mai. Misali idan aka tona mai a Jihar Borno a fada min ta ina za a fita da shi zuwa kasar waje? Hanyar da za a fita da shi domin sayarwa ita ce matsala.
Me za ka ce game da karancin wutar lantarki da ya addabi kasar nan?
Rashin wutar lantarki na daya daga cikin abubuwan da suka gurgunta tattalin arzikin Najeriya, duk kasar da take fama da karancin wutar lantarki a duniya babu ci gaban da za ta samu domin kamfanoni masu zaman kansu suke magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin al’umma ba su da wutar da za su yi amfani da ita dole sai sun yi amfani da man dizal. Kayan da suka sarrafa kuma zai yi matukar tsada a kasuwanni domin da janareta suke amfani wajen sarrafa kayayyakin kamfanin. Saboda haka nake cewa Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su dage sosai wajen magance wannan matsala da take ci gaba da addabar ’yan Najeriya, duk inda ka je a halin yanzu ana fama da karancin wutar lantarki a kasar nan.
Mene ne sakonka ga ’ya’yan Jam’iyyar PDP?
Babban sakona shi ne su ci gaba da yin hakuri, domin yanzu kowa ya san abubuwan da SUke faruwa na talauci da tsadar kayan abinci a kasuwanni. Lokacin mulkin PDP kowa ya ga ci gaban da aka samu daidai bakin gwargwado, za mu sake kafa gwamnati a Najeriya.
A karshe mene ne sakonka ga jama’ar kasa?
Duk lokacin da na zanta da manema labarai nakan ce idan an ji na yi kuskure a kira ni a fada min domin babu wanda ya wuce ya yi kuskure a rayuwa, wannan shi ne sakona.
A matsayina na tsohon malamin makaranta ina da dimbin dalibai a ciki da wajen kasar nan masu karanta wannan tattaunawa a cikin wannan jarida mai albarka ta Aminiya.