Jam’iyyar PDP za ta sake kwace karamar Hukumar Lere
Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Alhaji Tasi’u Bala Agaji ya ce Jam’iyyar PDP za ta sake kwace karamar hukumar daga hannun Jam’iyyar APC.Alhaji Tasi’u Bala ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, bayan da akasake zavensa a matsayin shugaban jam’iyyar na karamar hukumar, inda ya ce […]
Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Alhaji Tasi’u Bala Agaji ya ce Jam’iyyar PDP za ta sake kwace karamar hukumar daga hannun Jam’iyyar APC.
Alhaji Tasi’u Bala ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, bayan da aka
sake zavensa a matsayin shugaban jam’iyyar na karamar hukumar, inda ya ce za su sake karve karamar hukumar ne saboda jama’ar yankin sun gane cewa PDP jam’iyya ce mai adalci.
“Dukkan wakilan da aka zava a karamar hukumar a karkashin Jam’iyyar APC, sun gudu sun bar jama’ar da suka zave su. Ba su yi wa al’ummar komai, don haka da yardar Allah za mu sake karve karamar hukumar. Domin magoya bayan APC, sun ce gara mulkin baya da mulkin da ake gudanarwa yanzu a karkashin Jam’iyyar APC,” inji shi.
Alhaji Tasi’u Bala ya ce babu shakka jam’iyyarsu ta PDP ta samu matsaloli a baya, kan irin nade-naden da aka rika yi maimakon zave. Ya ce wannan ne ya haifar musu da rashin cin zave a zavuvvukan da aka gudanar a baya.
Ya ce amma daukar matakin barin ’ya’yan jam’iyya su zavi wadanda suke so, a matsayin shugabanninsu ya kara wa jam’iyyar martaba a karamar hukumar a yanzu.