Jam’iyyar Republic ta mamaye majalisar dattijan Amurka
Jam’iyyar Republican ta kasar Amurka ta lashe zaben tsakiyar zango da aka gudanar, inda ta samu dimbin kuri’u a jihohin Amurka da suka hada da Arkansas da Colorado da Iowa da Montana da North Carolina da South Dakota da West birginia, inda a halin yanzu Shugaban ’yan Republican Mitch McConnel zai zama shugaban zaman majalisar. […]
Jam’iyyar Republican ta kasar Amurka ta lashe zaben tsakiyar zango da aka gudanar, inda ta samu dimbin kuri’u a jihohin Amurka da suka hada da Arkansas da Colorado da Iowa da Montana da North Carolina da South Dakota da West birginia, inda a halin yanzu Shugaban ’yan Republican Mitch McConnel zai zama shugaban zaman majalisar.
Wannan nasara da jam’iyyar Republican ta samu, Amu8rkawa sun yi murna matuka, indaa sakon taya murka da shugaban jam’iyyar, Reince Priebus ya aike ya yi nuni da cewa, ‘amurkawa sun bayar da amanarsu ga jam’iyyar Republican.’
Baya ga nasarar da jam’iyyar ta samu a majalisar dattijan Amurka, tana yunkurin mamaye majalisar wakilan kasar, ibnda ta ci gaba da rike kujerunta na jihohin da suka hada da Alabama da Georgia da Kansas da Maine da Mississippi da Nebraska da Oklahoma da South Carolina da Tennessee.
Duk da wannan nasarar da Republican ta samu, ta fuskanci turjiya a jihohin Florida da Wisconsin, inda gwamnoninsu suka sha da kayar.