Jam’iyyu 45 sun marawa dan takarar Gwamnan APC a Gombe baya

Jam’iyyun adawa 45 a jihar Gombe karkashin gamayyar hadakar jam’iyyu ta IPAC sun amince da marawa dan takarar Gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar APC Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya baya a zaben da za a yi ranar Asabar. A wata sanarwa da shugaban IPAC ya fitar na cewa, sun yanke shawarar marawa dan takarar Gwamnan APC […]

Jam’iyyu 45 sun marawa dan takarar Gwamnan APC a Gombe baya

Jam’iyyun adawa 45 a jihar Gombe karkashin gamayyar hadakar jam’iyyu ta IPAC sun amince da marawa dan takarar Gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar APC Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya baya a zaben da za a yi ranar Asabar.

A wata sanarwa da shugaban IPAC ya fitar na cewa, sun yanke shawarar marawa dan takarar Gwamnan APC baya ne bayan ganawar da suka yi da sauran jam’iyyun adawa.

Wasu daga cikin jam’iyyun da suka marawa Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya baya sun hada da: Accord Party, DPP, ADC ACD, AD, MPN, CAP, BNPP, APA, AA, MMN, ANP, PPC, HDP, UPN, NCP, UPP, NCMP da PAC da dai sauransu.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta