Jam’iyyu PDP da APC sun gaza – Musalla
Alhaji Sadeek Ibrahim Musalla tsohon Shugaban Riko na kasa na Jam’iyyar APGA ne kuma a yanzu shi ne Sakataren Jam’iyyar United Progressibe Party, (UPP) na kasa. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya ce ’yan Najeriya sun gaji da jam’iyyun PDP da APC saboda ba su cika alkawuran da suka yi musu ba: […]
Alhaji Sadeek Ibrahim Musalla tsohon Shugaban Riko na kasa na Jam’iyyar APGA ne kuma a yanzu shi ne Sakataren Jam’iyyar United Progressibe Party, (UPP) na kasa. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya ce ’yan Najeriya sun gaji da jam’iyyun PDP da APC saboda ba su cika alkawuran da suka yi musu ba:
Wadanne shirye-shirye kuke yi don tunkarar zabubbukan 2019?
Abubuwan da muka sanya a gaba su ne rajistar wadanda za su yi mana takara a zabubbuka masu zuwa a badi. Ko a makon jiya, akwai Mista Daniel Akinlami wanda ya zo ya nemi mu ba shi dama ya tsaya takarar Shugaban kasa a karkashin wannan jam’iyya. Kuma akwai Farfesa Moghalu wanda shi ma ya bukaci mu ba shi dama ya yi takarar Shugabancin kasar nan. A takaice muna da ’yan takara da dama ta kujerar Shugaban kasa da gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da majalisun jihohi, da muke ta yin rajistarsu.
Kana ganin sabuwar jam’iyyar taku ta UPP, za ta yi tasiri a zabubbukan 2019?
Babu shakka Jam’iyyar UPP za ta yi tasiri a zabubbukan 2019. Domin idan ka dubi Jam’iyyar PDP jama’ar Najeriya ba sa yayinta yanzu. Haka ita ma Jam’iyyar APC jama’a sun dauka daga zuwanta, za a samu canjin da ake bukata. Amma a gaskiya zuwa yanzu ba a samu wannan canji da ake bukata ba. Wannan ya sa jama’a suna neman sababbin jam’iyyun da za su tafi.
Jam’iyyun APC da PDP sun gwada rawarsu amma jama’a ba su gamsu da rawar da suka taka ba. Kuma ko a kwanakin baya idan ka dubi rawar ganin da wannan jam’iyya ta UPP ta taka a zaben Gwamnan Jihar Anambara a cikin jam’iyyu 37 da suka shiga takara jam’iyyarmu ce ta zo ta 4. Duk da irin magudin da aka yi.
A takaice mene ne manufofin wannan jam’iyya?
Manufar wannan jam’iyya ita ce kawo canji na gaskiya a Najeriya. Saboda abubuwan da suke faruwa sun sanya mutane da dama suna nuna kosawarsu da irin tafiyar da gwamnatin ke yi a Najeriya. Saboda haka suke neman, a kawo jam’iyyar da za ta kawo canji na gaskiya. Domin yanzu idan ka dubi maganar yaki da cin hanci da rashawa da ake yi a Najeriya. Har yanzu babu wani canji da aka samu. An kama mutane da dama an ce sun yi sata, amma har yanzu an kasa hukunta su. Yanzu idan kana tafiya a Najeriya kana kallo za ka ga yadda jami’an tsaro suke karbar kudi a wurin jama’a a kan hanyoyin kasar nan. Duk wadannan abubuwa ne da suka kamata a ce an samu canji a kansu. Don haka dole ne a samu canji na gaskiya a Najeriya.
Yaya kake kallon yadda yanayin siyasa yake tafiya a kasar nan a yanzu?
Siyasa tana sake salo a Najeriya. Domin misali abubuwan da suka fara fitowa na ’yan majalisar kasar nan, yanzu jama’a da yawa suna son a soke Majalisar Dattawa a bar Majalisar Wakilai kadai. Ni kaina na goyi bayan a soke Majalisar Dattawa domin suna aiki iri daya ne da Majalisar Wakilai. Saboda haka mu ma lokaci ya yi da za a soke Majalisar Dattawa a Najeriya.
Yaya kake kallon rikice-rikicen Fulani makiyaya da manoma da ake fama da su a kasar nan?
Wato rikice-rikicen Fulani makiyaya da manoma abu ne da aka fara yin su tun iyaye da kakanni. Amma ba a taba mayar da shi siyasa ba, sai a wannan lokaci na gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari. Kuma wadanda suka mayar da wadannan rikice- rikice na siyasa, sun ga babu hanyar da za su iya hana wannan gwamnati sakewa, sai ta wannan hanya. Saboda Shugaban kasa Buhari Bafulatani ne.
Wann sako kake da shi ga ’yan Najeriya musamman ganin yadda zabubbukan badi suke kara gabatowa?
To abin da nake son jama’a su fahimta, shi ne su tantance mutanen da za su zaba a wadannan zabubbuka masu zuwa. Domin Hausawa sun ce auren baya, sadakin na gaba. Don haka mu duba mutanen da muka zaba a baya, shin sun yi mana ayyukan da suka ce za su yi. Idan ba su yi mana ba, mu sake tantance wadanda za mu sake zaba. Domin mu samu mutanen da za su taimaka wajen gyara kasar nan.