Jam’iyyun APC da PDP a Katsina sun mayar da hamayyarsu kafofin sada zumunta

Jam’iyyar APC mai mulki da abokiyar hamayyarta ta PDP a jihar Katsina sun sake matsa kaimin kamfe a kafofin sadarwa don jawo ra’ayin jama’a su mara musu baya. Aminiya ta lura cewa a kwanannan akwai karin hamayyar siyasa a tsakanin jam’iyyun biyu inda suka rika amfani da sunaye daban-daban don dakile junansu su sami karin […]

Jam’iyyun APC da PDP a Katsina sun mayar da hamayyarsu kafofin sada zumunta

Jam’iyyar APC mai mulki da abokiyar hamayyarta ta PDP a jihar Katsina sun sake matsa kaimin kamfe a kafofin sadarwa don jawo ra’ayin jama’a su mara musu baya.
Aminiya ta lura cewa a kwanannan akwai karin hamayyar siyasa a tsakanin jam’iyyun biyu inda suka rika amfani da sunaye daban-daban don dakile junansu su sami karin magoya baya a zabe mai zuwa.
Kullum jam’iyyun suna caccakar juna tare da kushewa da yabon kansu ta kafofin sadarwa na Facebook da whatsapp da tiwiter da sauransu don samun karin magoya baya.