Jam’iyyun PDP da APC da Accord sun yi gangami rana daya a Ibadan

Jam’iyyun  PDP da APC da Accord, masu adawa da juna, sun gangamin magoya bayansu rana daya a Alhamis din makon jiya a birnin Ibadan, inda tsohon Gwamnan Jihar  Oyo,  Adebayo Alao Akala, ya bayyana kansa, domin sake dawowa bisa kujerar Gwamnan jihar. A wannan rana ne dai dimbin magoya bayan  Jam’iyar ACCORD  suka gudanar da […]

Jam’iyyun PDP da APC da Accord sun yi gangami rana daya a Ibadan
Jam’iyyun PDP da APC da Accord sun yi gangami rana daya a Ibadan

Jam’iyyun  PDP da APC da Accord, masu adawa da juna, sun gangamin magoya bayansu rana daya a Alhamis din makon jiya a birnin Ibadan, inda tsohon Gwamnan Jihar  Oyo,  Adebayo Alao Akala, ya bayyana kansa, domin sake dawowa bisa kujerar Gwamnan jihar.
A wannan rana ne dai dimbin magoya bayan  Jam’iyar ACCORD  suka gudanar da addu’ar sadakar kwanaki bakwai da rasuwar mahaifiyar jagoransu, tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Rashhed Ladoja.
Wakilin Aminiya ya ga yadda aka  yi ta fargabar barkewar tarzomar siyasa a tsakanin magoya bayan wadannan jam’iyu uku, masu hamayya da juna da suka gudanar da tarukansu a wurare daban-daban cikin birnin Ibadan. Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Oyo, ta girke ‘yan sandan kwantar da tarzoma, dauke da bindigogi da motoci masu yayyafin ruwan zafi da dawakai da karnuka  a wuraren da aka gudanar da wadannan tarukan siyasa guda uku, domin guje wa tashin hankali.
 Birnin Ibadan, hedkwatar Jihar Oyo, a wannan rana ya cika, ya batse da dubun magoya bayan Jam’iyun siyasa guda uku, wato APC da ke mulki a jihar da PDP da ACCORD, masu adawa, wadanda shugabanninsu suka jagoranci magoya bayansu da suka shafe yinin wannan rana suna taro a wannan birni mafi girma a nahiyar Afrika.
A yayin da babban zauren taro na Premier Hotel ya karbi bakuncin taron shugabannin Jam’iyyar APC na jihohi shida a Kudu maso Yammacin kasa.
 Ita kuwa Sakatariyar jam’iyar PDP da ke Dandaru, cika tayi, ta batse da magoya bayanta da suka halarci bikin fitowar tsohon Gwamnan jihar Otunba Christopher Adebayo Alao Akala, wanda ya nuna sha’awar sake dawowa bisa kujerar gwamna a zaben shekara ta 2015.
Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Rasheed Ladoja, shi ya jagoranci ’ya’yan jam’iyarsa ta ACCORD zuwa wajen taron addu’ar sadakar kwanaki bakwai da rasuwar mahaifiyarsa, Alhaja Alimat Sadia Ladoja, da aka gudanar a dandalin Kulob din Recreation, a Ibadan.
Gwamnoni biyu da suka halarci taron jam’iyar  APC a Ibadan, wato, Sanata Abiola Ajimobi na Jihar Oyo da takwaransa na Jihar Osun Rauf Aregbesola, da wasu jiga jigan jam’iyar PDP da suka hada da Alhaji Yekini Adeojo da Sanata Ayo Adeseun, sun bayar da mamaki a lokacin da aka hangesu a wajen taron addu’ar sadakar bakwai na rasuwar mahaifiyar tsohon Gwamna Rashhed Ladoja, wanda shi ma yake son sake dawowa bisa karaga a karkashin inuwar jam’iyarshi ta ACCORD a zaben shekara ta 2015.
Zargin da PDP tayi wa APC na shirya munakisa da za ta janyo koma-bayan gangamin sake fitowar tsohon Gwamna Adebayo Alao Akala, bai yi tasiri a wannan rana ba, domin an gudanar da taron lafiya. Da take kare kanta dangane da wannan zargi, jam’iyar APC mai mulki a jihar, cewa tayi ta riga ta gano shure-shure PDP take yi, wanda ba zai hana ta mutuwa ba. Kuma yin hakan, ba zai zame mata barazanar zaben badi ba.
Jim kadan bayan zagaya sassa daban-daban na birnin Ibadan, a cikin wani jerin gwanon motoci, tsohon Gwamna Adebayo Alao Akala, na jam’iyar PDP, wanda ya sha kaye a zaben 2011, ya ce, bayan shiga cikin sako-sako a wannan birni, ya fahimci cewa, mutane suna cikin wani irin hali na damuwa, wanda ya yi musu alkawarin kyautata rayuwarsu a wannan dawowa bisa karagar mulki da yake so idan ya samu.
Ya ce, shi bai ga dalilin kalubalantar shirye-shirye da ayyukan da gwamnatin APC ke yi a jihar ba, a maimakon haka zai mayar da hankali ne wajen tunanin yadda zai taimaka wajen shawo kan irin matsalolin da dimbin jama’a ke fuskanta.