…Jamus da Birtaniya na kyamar kakaba wa Rasha takunkumi
Ministan Harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, tun a ranar Lahadin da ta gabata ya gargadi kan hadarin da ke tattare da kaurace wa Rasha a taron kasashe takwas (G8) da suka karfin masana’antu a duniya, wanda aka shirya gudanarwa a Sochi da ke kasar Rasha.Ya yi wannan gargadin ne a daidai lokacin da Sakataren Harkokin […]
Ministan Harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, tun a ranar Lahadin da ta gabata ya gargadi kan hadarin da ke tattare da kaurace wa Rasha a taron kasashe takwas (G8) da suka karfin masana’antu a duniya, wanda aka shirya gudanarwa a Sochi da ke kasar Rasha.
Ya yi wannan gargadin ne a daidai lokacin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry ya yi barazanar cewa Gwamnatin Mosko za ta rasa kujerarta a kungiyar kasashen masu karfin masana’antu, saboda rikicin Ukraine.
“kungiyar G8 ita ce kawai kafar da ke bai wa kasashen Turai yin huldar kai tsaye da kasar Rasha, don haka mu yi nazari kan mun iya wancakalar da wnanan damar?” a cewar Steinmier, lokacin da aka yi wata tattaunawa da shi a gidanin Talabijin din Jamus na ARD.
Steinmeier ya ce akwai bukatar shugabannin kasashen duniya su yi muhawara a wannan makon, amma su yi takatsantsan kan matakin da za su dauka don gudun rura wutar rikici.
“Ina ganin dole ne mu bayar da gudunmuwarmu wajen hana ruruwar wutar rikicin Ukraine,” inji shi.
Sabanin Amurka da Rasha, kasar Jamus ba ta cikin kasashe masu fada a ji a Majalisar tsaro ta Majalisar dinkin Duniya.
Ita kuwa kasar Birtaniya na adawa da kakaba wa Rasha takunkumin tattalin arziki a kan kasar Ukraine, kamar yadda rahoton kafafen yada labarai ya bayyana, tun a Talatar da ta gabata, inda suka tsakuro bayanai daga wasu takardu da aka fito da su daga fadar mulki ta Downing Street.
Takardun bayanan, an dauki hotonsu ne a hannun wani babban jami’in gwamnati, wanda ke tafiya don ganawa da Firayiminista, Dabid Cameron, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC da jaridu da dama suka bayyana.
Matsayin Birtnaiya kan rikicin Ukraine ya bayyana karara, inda aka gano cewa: “Gwamnatin Birtaniya ba za ta amince da kakaba takunkumin ciniki, ko kuma rufe cibiyoyin hada-hadar kasuwancin Landan da ke kasar Rasha.”
A birnin Landan mafi yawan attajiran Rasha ke hada-hadar kasuwanci da sarrafa dukiyarsu a bankuna da kasuwannin hannun jari. Don haka idan Birtaniya ta amince da takunkumin, kasar za ta shiga cikin jerin wadanda za su yi asara.