Jamus da Gidauniyar Bill Gate za su taimaka da Yuro miliyan 2 don noman shinkafa
Gwamnatin Jamus da tallafin Gidauniyar Bill da Melinda Gates sun samar da Yuro miliyan biyu don tabbatar da kashi na biyu na shirin noman shinkafa a Najeriya, mai taken Comparatibe African Rice (CARI) Daraktan shirin na, CARI, Mista Jean Bernard Lalannehe, ya ce shirin karo na biyu da ake kira CARI-2 za a aiwatar da […]
Gwamnatin Jamus da tallafin Gidauniyar Bill da Melinda Gates sun samar da Yuro miliyan biyu don tabbatar da kashi na biyu na shirin noman shinkafa a Najeriya, mai taken Comparatibe African Rice (CARI)
Daraktan shirin na, CARI, Mista Jean Bernard Lalannehe, ya ce shirin karo na biyu da ake kira CARI-2 za a aiwatar da shi ne a jihohin Kebbi da Kaduna da kuma Jigawa.
A cewarsa manufar shirin ita ce a taimaka wa kananan manoma su samu karin kudaden shiga don samar wa iyalansu da kasa baki daya ingantacciyar shinkafa.
Ya kara da cewa shirin na ‘CARI’ an kaddamar da shi ne a kasashe hudu na Afirka da suka hada da Najeriya da Burkina Faso da Ghana da Tanzaniya a shekara ta 2013.
Shirin na Hukumar Bunkasa Tattalin Arzikin ta gwamnatin kasar Jamus ne tare da tallafin kudi daga Gidauniyar Bill da Melinda Gates na kasar Amurka.
Lalannehe, ya ce Ma’akatar Aikin Gona da Bunkasa Karkara da ta kaddamar da shirin na CARI-2 ya ce shirin ya faro ne daga watan Yunin bara, kuma ana sa ran zai kai Yunin shekarar 2021.
Har ila yau a cewar sa, shirin zai fi mayar da hankali ne kan kasuwancin shinkafa don tabbatar da masu sarrafa ta suna da alaka ta kai-tsaye da ’yan kasuwa da masu sarrafa ta da ma masu casarta da kuma masu zazzabarta da kuma dillalan irinta.
Daraktan ya kara da cewa an bi hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar sayar da shinkafar da ake sarrafawa a duk fadin Najeriya.