Jamus ta sallami kociyanta Hansi Flick
An bai wa Rudi Voller aikin riƙon ƙwarya.
Hukumar kwallon kafa ta Jamus ta sallami kociyanta, Hansi Flick, saboda abin da ta kira rashin taka rawar gani daga bangarensa.
Sallamar Hansi Flick na zuwa ne bayan da Japan ta doke ƙasar da 4-1 a wasan sada zumunta.
- Kotu ta sake soke nasarar wani dan majalisar NNPP daga Kano
- Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutum 15 a Adamawa
Ya zama koci na farko da aka kora a matakin mai horar da tawagar ƙasar tun lokacin da aka ƙirƙiri aikin a 1926.
Flick mai shekara 58 wanda ya ja ragamar wasa 25 tun bayan da ya maye gurbin Joachim Low a Agustan 2021, ya yi rashin nasara a wasa huɗu daga biyar da ya buga.
An bai wa Rudi Voller aikin riƙon ƙwarya, wanda ya ja ragamar tawagar daga 2000 zuwa 2004.
Jamus ce za ta karɓi baƙuncin gasar Kofin Nahiyar Turai da za a yi a cikin shekarar 2024.
Flick, shi ne mataimakin Low a tawagar Jamus tsakanin 2006 zuwa 2014.
Ya fara da cin wasa takwas daga baya abubuwa suka ɓalɓalce wa tawagar, wadda aka yi waje da ita a karawar cikin rukuni a kofin duniya a Qatar a 2022.
Cikin wasa 12 da tawagar ta Jamus ta buga ta yi nasarar doke Oman da Costa Rica da kuma Peru.