Jamus za ta bunkasa watur lantarkin Najeriya ta hanyar hasken rana – Jakadan Jamus

kasar Jamus ta ce, ta fara gudanar da aikin kafa injinan samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da hasken rana a sassa da dama na kasar nan. Jakadan Jamus a Najeriya, Micheal Zenner, ya yi furucin ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron da cibiyar horar da daraktoci ta (IOD) ta […]

Jamus za ta bunkasa watur lantarkin Najeriya ta hanyar hasken rana – Jakadan Jamus
Jamus za ta bunkasa watur lantarkin Najeriya ta hanyar hasken rana – Jakadan Jamus

kasar Jamus ta ce, ta fara gudanar da aikin kafa injinan samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da hasken rana a sassa da dama na kasar nan.

Jakadan Jamus a Najeriya, Micheal Zenner, ya yi furucin ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron da cibiyar horar da daraktoci ta (IOD) ta shirya a Abuja, wanda ta yi masa lakabi da (Harkokin Kasuwanci a Najeriya).
Ya ce, a yanzu haka ana gudanar da aikin a jihohi uku da suka hada da Jihar Sakkwato da Neja da Kuros Riba da kuma Bauchi.
Ya bayyana cewa tuni aka kafa kwamitin kwararru da injiniyoyi wadanda za su rika sanya ido a aikin.
Ya kara da cewa tuni ana ci gaba da gudanar da nazari don gano inda wuraren da za su fi dacewa da kafa injinan.
“Tuni jami’anmu da ke bangaren harkokin ci gaba suka fara gudanar da aiki a jihohin Sakkwato da Neja da Kuros Riba da kuma Bauchi. Mun kafa kwamitin kwararru da injiniyoyi wadanda suke gudanar da bincike don gano inda zai dace a sanya injinan samar da wutar,” inji shi.
Ya bayyana cewa aikin yana daya daga cikin damarmakin da aka samu wajen samar da wutar lantarki a Najeriya.
A nasa jawabin, shugaban Cibiyar Daraktocin, reshen Abuja, Cif Red Onyeabo, ya bayyana taron a matsayin wata kafa mai muhimmanci da daraktocin ke haduwa don tattauna harkokin kasuwanci a junansu.
Ya ce, daya daga cikin manufofin cibiyar shi ne ta ilimantar tare da tabbatar da jagoranci nagari.
Daga nan sai ya yaba wa kasar Jamus dangane da aikin samar da wutar lantarkin da take yi.
Ya bayyana cewar karancin wutar lantarki yana daya daga cikin kalubalen da ke ci wa masana’antu tuwo a kwarya.
Ya bayyana cewa idan aka kammala aiki zai yi maganin kalubalen da kasar take fuskanta ta bangaren wutar lantarki.