Jan-bakin jabun dan magori
Jan-bakin jabun dan magori Magungunsa sun jefa jama’a garari Waraka an sa mata sasari Lange-lange na sanya zazzabin zabari Zogi radadi na zunguri Hukumar inganta uwar jikin duniya Ta koka da hayaniyar kassara lafiya A fadin saharar Ifrikiyya Shi ya sa na fasa kwai mai gunya Hada-hadar cutar al’umma da zamiya Jami’ar Edinburgh […]
Jan-bakin jabun dan magori
Magungunsa sun jefa jama’a garari
Waraka an sa mata sasari
Lange-lange na sanya zazzabin zabari
Zogi radadi na zunguri
Hukumar inganta uwar jikin duniya
Ta koka da hayaniyar kassara lafiya
A fadin saharar Ifrikiyya
Shi ya sa na fasa kwai mai gunya
Hada-hadar cutar al’umma da zamiya
Jami’ar Edinburgh
Tai binciken jike-jiken bogi
Sayun da ke haifar da zogi
Mutum ya ji kamar ya tsunduma a kogi
Jamusawa na kyarar bedbug a Bedburg
Masu fasa-kwauri
Na yi wa kasuwanci kawari
An illata mutanen gari
Masu kange kofa da asabari
Babu ragar sangen shamakin fari
Hukuma tai kuduri
Na bankado bata-gari
Masu sara da gatari
Da ke hana al’umma cin jinbiri
Amai da gudawa na makari
daurewa kundukuki
Maganin maiko da zaki
Jijiyoyi sun zama taurikiki
Doron baya kamar alkuki
Jikkata jin jikin duka da kulki
Dala kofar hanci gashin balama
Hada-hadar da ta haifar da hauma-hauma
Rudanin rashin makama
Haurobbiyawa maganin bogi ya kankama
Asarar dukiya ta samu gindin zama
Birnin Shehu
Babu mai kashe taro da ahu
Don tattare dodon kodi a buhu
Kar ya kassara mafitsara da huhu
Jaye-jayen jenten huhuhun ma’ahu
Hanta da koda
Laulayin borin na-kada
Busasshiyar fatar kaushin kada
Inna uwa ta shanye gabobin gada-gada
A gaza tsere mata da takun gada
Haurobiyawa ai tsafta
Kula da muhalli a fafata
Sharar tsintsiya kada a kakkauta
Baban-burin-huriyya fafari masu mugunta
Fatanmu dai Imani ya inganta
Hukumar Inganta uwar jikin al’umma
Ta fasko jirgin masu zalama
Da ke saye da sayar da kunama
Dala kofar hanci da zagaye gashin balama
Sun cutar da jama’a cikin lalama
An fasko masu hada-hadar curin kwayoyin magungunan bogi da jike-jike har na Dala gashin balama kofar hanci da zagaye, al’amarin da Hukumar Ingantan uwar jikin al’ummar duniya ta hakakke cewa ana tsuwurwurta wannnan haramtaccen kasuwanci a fadin saharar Ifrikiyya. Kuma masu fasa-kwauri da hada-hadar kasuwancin bayan fage sun tabbatar da cewa suna yin cinikinsu ne don yin gasa da KAFAdA-KYAMIS, wato mai tallafar daurin magunguna a kafada yana kara-kaina a kwaro-kwaro da gararamba a tituna don jinka wa al’umma su kwankwada, su difara masa abin hasafi.
Magungunan bogi dai an tabbatar su ke kara ta’azzara radadi da zogi, har mutum yan ji kamar ya tsunduma cikin kogi lokacin da ake fama da magagi. Binciken da ya fasko jirgin masu jirga uwar jikin al’umma a wannan yanki na duniya, musamman kasar Haurobiya an aiwatar da shi ne a tsakanin shekaruin dubu karamin lauje da kwanciyar magirbi zuwa dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama. Kuma Jam’in jama’ar jami’ar Edinburgh ne suka yi aiki tukuru wajen bankado dimbin magungiunan bogi da ke shawagi a sansanin saharar Ifirikiyya, inda Jabun dan magori ke nuna wa al’umma kiyayya.
Batu na ingarman karfen karafan titin tarragon kwangirin layin dogo, a daukacin lokutan wulwulawar agogo, in an aka tunttubi gwagggo kan yadda ake yi magani ya makkale mata a kogo, tabbas za ta iya cewa sakacin Hukumar NA-FI-DAKIN cewa, tunda ita aka dora wa alhakin tabbatar da inganci nau’ukan jike-jiken magunguna da kayan dundume kurruru, amma sai ta zuwa na-mujiya kuru-kuru!
Baya ga illar da al’umma ke yi wa kanta da kanta, musamman wajen gyara magudanan ruwa da kwatoci, har zuwa ga amfani da sangen sage shawagin lange-lange mai ramar keta, to ba sa nusar da hukuma illar magungunan bogi. Kuma tun bayan da marigayiya MACE MAI KUNYA DA KWALLI ta daina jan ragamar Hukumar NA-FI-DAKIN aka yi ta samun tarnaki da koma-baya, har ta kai ga magungunan bogi sun karade kasuwanni, ammma an tsahirta ana ta wuni-wuni a cikin kowane yini.
Su kuwa jami’an hukumar kula da ingancin uwar jikin Haurobiyawa sun dade da kwasar gararuma, inda suka bar al’umma na ta dama-dama da dawurwurrin rashin makama ballantana makoma. Hasali ma dai a farfajiyar Makarantar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, mun taba bankado batun inshorar kula da uwar jikin jama’ar kasar nan, inda aka nusar da al’umma yadda aka karke da SHARbAR SHAWARMAR SHIRWA SHIRU!
Ga shi kafafen yada kwakwazo na ta yamadidi da cin kasar Bokayen Turai da suka yi warwas a wasattsaken jarabawa. To wane ne, ba wane ne ba?
Matukar gwamantin kasar nan ta ki yin katabus bisa wannan rahoto, to za mu yi kira ga BAKULE mai kulle-kullen INA-DA-DURWAN-KOLO da BARAROJI da ’YAR MAI GANYE da daukacin masu ikrarin sanin yadda ake sarrafa magungunan gargajiya kan lallai su bunkasa dabarun sarrafa sabara da kirya da danya da sauran nau’ukan sayu da kaucin itatuwa, su fantsama cikin al’umma a yi ta hada-hada, wanda ya kwankwada ya samu waraka ko akasin haka shi ya jiwo.
Hakika lokaci ya yi da za a zaburar da al’umma su Ankara kafin magungunan bogi su kassara su, bayan sun haifar musu da asarar dimbin dukiya. Uwa-uba, gwamnatin Baban-burrin-huriyya ta kara kaimi wajen samar da managartan curin kwayoyin magani da jike-jike a farashi mai rahusa, tare da bai wa majinya kayan dundume kururu kyauta-kyauta, musamman lokacin da suka yi rashe-rashe a karagar kula da wadanda suka lula a lawlawar laulayi a farfajiyar Bokan Turai. Sannan a tabbatar an bi kadin rahoton Jam’in jama’ar Jami’ar Edinburgh, wanda ya fasko jirgin masu hada-hadar gurbatattun magunguna don jirgawa da jijjiga jama’ar Haurobiya da daukacin fadin Ifirikiyya.