Jan hankali ga al’umma game da zaben 2015

Malam Muhammad dandattijo, Bayan NEPA Malumfashi (07039018940), a nasa tsokacin, yana cewa:Duk wani mai hankali da ke da kishi da kyakkyawar manufa ga Najeriya da ’ya’yanta, yana son ganin cewar al’umma, musamman ma talakawa wadanda suke cikin halin tsaka mai wuya, halin rashin tabbas na sanin makomarsu da ta kasarsu ta haihuwa. Sun samu jagoranci […]

Jan hankali ga al’umma game da zaben 2015
Jan hankali ga al’umma game da zaben 2015

Malam Muhammad dandattijo, Bayan NEPA Malumfashi (07039018940), a nasa tsokacin, yana cewa:
Duk wani mai hankali da ke da kishi da kyakkyawar manufa ga Najeriya da ’ya’yanta, yana son ganin cewar al’umma, musamman ma talakawa wadanda suke cikin halin tsaka mai wuya, halin rashin tabbas na sanin makomarsu da ta kasarsu ta haihuwa. Sun samu jagoranci nagari, ma’ana su samu shugabanni nakwarai, wadanda za su tabbar da abubuwan da ’yan Najeriya suka rasa, kamar doka da oda, tsayar da adalci a tsakanin al’umma ga mai mulki da wanda ake mulka, kawar da cin hanci da rashawa a ofisoshin gwamnati, da ma tsakanin al’ummar kasa, rashin tsaro wanda shi ne sanadiyyar asarar rayuka da ta dukiyoyi, sannan ga tashin hankula daban-daban a kasa.
Wadannan abubuwa sun sa Najeriya ta tsinci kanta a cikin balahirar da ba a san ranar fitar ta ba. kasashen da ake hangen sun ci gaba, abubuwan da suka tsare wa al’ummarsu ke nan, suka sa Allah Ya sa masu albarka a cikin shugabancin da suke, ’yan kasa suna son shugabanninsu, masu mulki kuma suna son talakawansu. Ba su fargabar su tunkari jama’arsu a kowane lokaci, saboda sun tsare masu hakkokinsu.
Ya ku ’yan uwana ’yan Najeriya, wannan shi ne muka rasa a kasarmu, shi ya sa na ga ya kamata in jawo hankalin ’yan uwana a game da zaben shekara ta 2015 da ya tunkaro mu, tun da an fara kada kugen siyasa a zahiri da sunan tarurrukan siyasa don hada kan ’yan jam’iyya da kuma karbar ’yan siyasa, wanda ya nuna a zahiri kamfen ake yi. Wanda ya nuna so ake a sake maimaita ’yar gidan jiya; ta hanyar yaudarar mu, ’yan siyasa da al’umma nakwarai; su saki jiki har a gama shirya makircin da ake shiryawa, don mayar da mu halin da muke ciki, ko kuma wanda ya fi shi muni.
Idan muka bari muka yi barci, ko muka sa ido ba mu dauki matakin gyara ba, wallahi wankin hula zai kai mu dare, daren da ba zai taba wayewa ba. Don haka ya zama wajibi mu sa ido wajen zaben mutanen da za su tsare mana hakkokinmu, tabbatar da gaskiya da adalci da doka da oda a tsakanin al’ummar kasa, wadanda za su kare mana dukiyoyinmu, rayukanmu da addininmu.
Duk dan takarar da ba zai iya kare mu daga bala’in da Najeriya take ciki ba na zubar da jinane kamar mayanka ba tare da hakkin shari’a ba da kuma iya kare dukiyoyinmu da addininmu ba, ya zama dole mu kyale shi. Mu sani cewa ya ku talakawan Najeriya, mafi yawan ’yan siyasarmu ba mu ne a gabansu ba, mafi yawancinsu manyan mayaudara ne na sara da gatari, wadanda ba Allah ne a gabansu ba, a’a me za su samu? Wace hanya za su bi su ci da guminmu ko muna so ko ba mu so. Irin wadannan ’yan siyasa suna samun goyan baya daga wasu daga cikin iyayen kasa.
Daga karshe, ina kira ga ’yan uwana ’yan Najeriya, ya kamata mu hankalta mu gane cewa an dade ana ruwa kasa na shanyewa, dole ne mu dauki matakin gyara ko don ’ya’yanmu da jikokinmu. Kuma muna jawo hankalin matasa wadanda da su wasu gurbatattu ke amfani ana kara gurbata siyasar Najeriya, ta hanyar ba su kayan maye, an hana masu aiki, an mayar da su karnukan farauta; bayan kuma kasarmu na da arzikin da za ta iya ba kowa aiki. Muna da albarkatun kasa, wanda ba sai mun dogara da fetur kadai ba, koda noma kadai mun iya rike kawunan mu. Ina kira ga matasa, a kula, a yi karatun ta natsu.