Jan hankali ga kungiyoyin Izala da Shi’a (1)
Wannan tsokaci mai take na sama, an gabatar da shi a shekarar 2014, shekara biyar ke nan da suka gabata. GIZAGO (08065576011) ya samo shi ne daga turakar hazikin marubuci, MALAM AUWAL KANO (08064595353). Muhimmancin abubuwan da aka tattauna ya sa aka bijiro da shi kuma ga abin da yake cewa: Gaisuwa da sallama […]
Wannan tsokaci mai take na sama, an gabatar da shi a shekarar 2014, shekara biyar ke nan da suka gabata. GIZAGO (08065576011) ya samo shi ne daga turakar hazikin marubuci, MALAM AUWAL KANO (08064595353). Muhimmancin abubuwan da aka tattauna ya sa aka bijiro da shi kuma ga abin da yake cewa:
Gaisuwa da sallama irin ta addinin Musulunci gare ku. Bayan haka, na yi niyyar amfani da wannan dama domin in jawo hankalinmu da tunatarwa da nasiha game da abubuwan da suke faruwa.
Gaskiya na lura ku ne matsalolinmu a yau. Duk wani rashin hadin kai da raba kan Musulmi, daga wajenku yake fitowa. Tsakaninku kowa kullum cikin zagin kowa yake. ’Yan Shi’a na fadin cewa ’yan Izala da Izalar kanta yaran Yahudawa ne kuma Yahudawa suka kirkire ta. ’Yan Izala na fadin cewa tushen Shi’a ya samo asali daga Yahudawa da Yahudanci. Har yau mun gaza gane tsakaninku wane ne mai gaskiya?
Musulunci da Musulmi a Najeriya ba abin da suke bukata sai hadin kai da zaman lafiya da girmama juna amma har yau kun kasa dinke wannan barakar, ta yadda za a samu ’yar fahimta a tsakaninku.
Mu dauki misali guda, mu Musulmi da ke nan Arewa kamar Kano, Katsina, Jigawa, Bauchi da sauransu; shin muna sane cewa har yanzu akwai ’yan uwanmu Hausawa wadanda ba Musulmi ba, ba kuma Kiristoci ba, su zallan Maguzanci suke yi? Idan ka shiga kauyukanmu, har yanzu ilimin aiwatar da ibada bai gama isarsu ba. Idan haka ne, yaya za ku tsaya zage-zage da kazafi wa junanku?
Gaskiya akwai bukatar sake lale da ya kamata ku yi, ku sani wadannan ’yan uwanmu da ke Maguzanci da Musulmin da ba su da ilimin aiwatar da yadda ibada take, suna da hakki a kanmu.
Game da Kungiyar Izala, gaskiya suna kokari wajen aikin musuluntar da Maguzawa, suna matukar kokari wajen shiga kauyuka da yada ilimin addinin Musulunci.
’Yan Shi’a, har zuwa yanzu ba ni da masaniya ko suna da makamancin irin kwamitocin da ’yan Izala suke da su na musuluntar da Maguzawa da yada ilimin addinin Musulunci. Idan babu, ya kamata ku yi. Ya kamata almajiran Zakzaki su sani, bukukuwa da suke yi ba shi ne Musulunci ba. Ya kamata su sani, babban jihadin da ya kamata su fara da shi, shi ne ceto Maguzawan da muke rayuwa tare da su da kuma ilimantar da ’yan uwanmu Musulmi da ba su gama fahimtar mene ne Musulunci ba. Domin shi jihadi daga tushe ake fara shi. Da fatan za a fahimce ni!”
***
Malam Auwal bai sha lalai da wannan tsokaci nasa ba, domin kuwa ya samu martanoni da dama kuma mabambanta, wadansu na goyon baya, wadansu kuwa akasin haka. Bari mu ga yadda za mu tsakuro wasu daga cikinsu:
Abdulhamid Muhammad Sani ya ce masa: “Amma dai a rubutunka ka gwada kana da gefe, abin da kuma ya saba ka’idar dan jarida ko marubuci!”
Shi kuwa Abba Buhari goyon baya ya yi tare da shawara, inda ya ce: “Allah Ya saka da alheri, fadakarwa mai kyau kuma mai amfani amma lokacin na gaba ka yi kokari ka rika yin kira ga kungiyoyin Musulmi baki daya, kada ka debi wasu; don sai in ga kamar ko’ina ana bukatar gyara kuma hakan kai ma zai sa kowa ya fahimce ka, ba tare da tunani biyu ba. Allah Ya sa mu dace, Ya amshi ibadojinmu, amin.”
Sai kuma Umma Rimaye, wacce ta bayyana cewa: “Amma in fa ta wajen shiga lunguna da kauyuka ne ana wa’azantar da mutane da nuna masu yadda za su kusanci mahaliccinsu, ’yan Izala na kokari a Najeriya.”
Shi kuwa Mustapha Ja’afar cewa ya yi: “Auwal, halal a bayyane take haka ma haram. Lallai dole a tausaya maka in har ka kasa gane daidai amma Allah Ya taimake ka ka gane gaskiya. Har abada karya da gaskiya ba za su taba haduwa ba in ma sun hadu to fa da sannu za su rabu. Wannan sabani da ka ga ana yi, har abada ba za a daina shi ba. Haka Allah Ya tsara, sai fa wanda Allah Ya yi wa jinkai. Allah Ya kashe mu cikin bin tafarkin Annabi (SAW).”
Ibrahim Daurawa ya shigo zancen da cewa: “To idan bakukuwan tuna ranar haihuwar wadanda Allah Ya ce a karbi addini a wajensu ba addini ba ne, mene ne matsayin abin da ka ce shi ’yan Shi’a kawai suke yi? Na zaci ma ka shiga cikin ’yan Shi’ar ka tambaye su ko suna da wani shiri irin wanda kake gani shi ne Musulunci, kafin ka dauki matsaya ko don gudun kada ka yi karya kana azumi. Sai ba ka yi hakan ba, saboda kana da wata manufa da kake son cimmawa. Shawarata gare ka, duk lokacin da za ka yi irin wannan rubutun naka, idan don Allah za ka yi, ya kamata ne ka binciki kowane bangare kafin ka zarge su. Kodayake na yarda ka dauki ’yan Shi’a mabiya Sayyid Zakzaky, don haka ma su ka ambata.”
Shi ma Rabi’u Aliyu Muhammad ga abin da yake cewa: “Allah Ya ba da lada. Haka yake, kamar yadda dan uwa ya yi karin tuni ga marubuci, idan za a yi jan hankali a kan Musulunci, a daina yin bangaranci, a rika kira ga kungiyoyin Musulmi baki daya. Allah Ya sa mu dace da ibadarmu.”
Shi kuwa Danladi Haruna karin haske ya yi da cewa: “Yan Shi’a na zuwa gidan karuwai wa’azi, domin su hana su zina, su koya musu Mut’a. Izalawa kuma na shiga kauyuka su hana kalankuwa, su samu kayan Zakka. Duk abin da aka ce masa kungiya yana tattare da son rai a ciki. Don haka a bar kame-kame, duk inda gaskiya take a bi ta ido rufe.”
Abdulhamid Muhammad Sani ya bijiro da ta’alikin cewa: “Auwal, ka sani kowace kungiya a kungiyoyin nan da yadda ta fahimci yadda za ta bi don kawo gyara. Misali: Wata itaciya ce ake son cirewa, wani sai ya hau kan itaciyar yana ciro kananan rassa kafin ma manya. Shi kuwa wani da ya zo sai ya fara tuttugar saiwar bishiyar.
“Abin da ’yan Buraza suka dauka ya yi kama da wanda ya fara tun daga saiwa. Su kuma ’yan Izala daga kankanan rassa. Wayar wa jama’a da kai da ’yan Buraza ke yi, na su san hakkinsu da kokarin kwatar hakkin daga mazalunta, a ganina ita ce hanya daya da za ta zama za a iya jawo sauran dukkan ’yan uwanmu. Kuma ka sani shi fa addini ba tilasci ba ne, imani ne da amincewa. In muka samar da kyakkyawan yanayi na shugabanci su da kansu za su zo don karbar Musuluncin. Amma ina amfanin masu ganin fahimtarsu ga Musulunci su kadai ke kan daidai?”
Za mu ci gaba